Dambaruwar shugabancin majalisa: Tsoron tsigewa ya sa Gbajabiamila ya dage zaman majalisa

Dambaruwar shugabancin majalisa: Tsoron tsigewa ya sa Gbajabiamila ya dage zaman majalisa

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila a yau Laraba ya ɗage zaman majalisar har zuwa wani lokaci saboda fargabar yiwuwar tsige shi da wasu yan majalisa ke kitsawa.

Gbajabiamila, wanda ya jagoranci zaman majalisar bayan hutun makonni, ya yi kira da a ɗage zaman saboda raɗe-raɗin tsige shi.

Ya jingina dage zaman ne kan horas da zababbun mambobin da ake yi a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labarai na Ƙasa ya tattaro cewa wasu ƴan majalisar sun kammala shirin tsige Gbajabiamila saboda ƙaƙaba dan majalisar wakilai Tajudeen Abbas da ya ke yi a matsayin dan takarar shugaban majalisar wakilan ta 10.

Wasu daga cikin ƴan majalisar da su ka zanta da NAN kan shirin tsigewar da aka yi da su, sun yi zargin cewa shugaban majalisar ya dage zaman ne saboda tsoron tsige shi.

Dan majalisa Ahmed Wase, mataimakin kakakin majalisar ya yi gaggawar nuna adawa da Gbajabiamila, ya na mai cewa babu buƙatar dage zaman kuma ba su amince ba.

Wase ya ce dage zaman bai dace ba; Ya kara da cewa za a iya haɗa horon da ake baiwa sabbin yan majalisa da kuma zaman majalisar.