Aljannu Sun Sumar Da Matan Amarya A Sakkwato

'Sai dai angon yayi kokari wurin ganin ya hana maza shiga cikin gidan sa lokacin da 'yan matan ke cikin hali na gushewar hankali. Saboda gujewar wata aika-aikar da zata iya faruwa. Mutanen da ke wurin sun yi al'ajabin wannan abin da ya faru yayin da duk suke tunanin cewa tabbas alokacin da 'yan matan da ke tsakiyar rawar su,da alamu sun sami ma su taya su rawar daga cikin aljannu,wadanda ke wurin sun tabbatar da yawan 'yan matan da suka suma ba su da matsalar aljanu,ance wannan ne karo na farko da suka shiga cikin wannan yanayi na suma sanadiyar aljanu.

Aljannu Sun Sumar Da Matan Amarya A Sakkwato
'Yan matan wata amarya a garin sifawa ƙaramar hukumar Bodinga Aljannu sun sumar da su a lokacin da suke tsaka da taka rawar murnar auren kawar su.
  Lamarin ya auku ne a ranar lahadi da misalin karfe takwas na dare, 'yan matan amaryar su kimamin goma sha biyu ne aljanun suka kifar.
Ranar asabar ce aka kai amarya dakinta, ranar lahadi da safe 'yan matan su kimamin sha biyu suka je gidan amaryar kamar yadda al'adar garin yake,sukan je gidan amaryar domin yin abinci.
'Yan matan sun yi abincin rana cikin kwanciyar hankali,sun dora na dare,sun kammala cikin nasara.
Bayan sun kare abincin daren sun dibarwa ango da sauran mutane;su ma sun zuba nasu sun ci, gama cin abincin kenan suka tayar da kida suka dinga tikar rawa abinsu.
Amaryar ma ba'abarta a baya ba,itama ta taya 'yan matan nata wannan shagalin,sai dai fara rawar da mintuna talatin kidan ya canja,yayin da masu rawar suka yi saurin canja takon rawar ta su.
  Shaidu tabbatace yace a lokacin da 'yan matan ke tsaka da taka rawa cikin 'yammatanci iskan budurci na kadawa da su,cikin jin karfin sabon jini, ganin dai suka yi wata yarinya ta fara faduwa, duk da haka ba su tsayar da kidan ba,suka ci gaba da rawar cikin kwanciyar hankali.
'Daga nan wasu 'yan matan na sake kifewa a some, hakan ma bai sanya aka dakata da rawar ba,bale ayi maganar kashe kidan.
Wasu 'yan matan su kamar uku sun sake biyar sawun somammin 'yan matan. Daga nan sai hankalinsu ya dan tashi,suka rage karar sautin kidan.
Ragowar 'yan matan da ke cikin hankalinsu,suma da guda-guda suka kama yanke jiki suna somewa a kasa.
Ganin haka ya sanya aka kashe kidan gaba daya tunda abin ya sauya daga rawa ya koma kamar filin tayar da bori.
Gida fa ya rude da yaruka kala-kala.
  Hakan dai akayi kokarin basu taimako na gaggawa ta hanyar yi mu su addu'o'i,amma duk da haka abin yaci tura,sai da aka gayyato iyayen su kowa yaje ya dauki 'yar sa.
  'Sai dai angon yayi kokari wurin ganin ya hana maza shiga cikin gidan sa lokacin da 'yan matan ke cikin hali na gushewar hankali. Saboda gujewar wata aika-aikar da zata iya faruwa.
Mutanen da ke wurin sun yi al'ajabin wannan abin da ya faru yayin da duk suke tunanin cewa tabbas alokacin da 'yan matan da ke tsakiyar rawar su,da alamu sun sami ma su taya su rawar daga cikin aljannu,wadanda ke wurin sun tabbatar da yawan 'yan matan da suka suma ba su da matsalar aljanu,ance wannan ne karo na farko da suka shiga cikin wannan yanayi na suma sanadiyar aljanu.
Zainab Aliyu sifawa.