Malamin addini ya shawarci sarakunan da Gwamnatin Sokoto ta cire su tafi kotu

Malamin addini ya shawarci sarakunan da Gwamnatin Sokoto ta cire su tafi kotu

Malamin addinin musulunci a Sakkwato Malam Murtala Bello Assada ya shawarci sarakunan da Gwamnatin Sakkwato ta cire wa rawani a satin nan su nemi haƙƙinsu a gaban Shari'a.
Malamin a wurin karatunsa da ya gabatar ya ce sarakunan su tafi kotu domin neman haƙƙinsu na ɓata masu suna da aka yi.
“Sarakuna ku taru ku kai shi kotu don bai da kowace hujja, in ka ce sarakunan da ka cire suna da alaƙa da bandit, ka cire su ka kuma kyale su ka ci amanar mutanen Sokoto, akai su kotu a kawo sheda, sarakuna APC ce ba su yi ba Gwamna ya cire su," kalaman Assada.