2023:Atiku Ne Yafi Cancanta A  Dukkan Masu Son Zama Shugaban Ƙasa-----Alhaji Auwalu Ila

Maganar goyon bayan Atiku ya aje Tambuwal ya ce "ita siyasa ra'ayi ce a gida guda ma za ka samu wani na PDP wani kuma yana APC balle maganar zaben dan takara, a 2019 Aminu Tambuwal  na goyi baya a Sakkwato yanzu kuma Atiku nake ra'ayi ina da hujjojina na yin haka, ina fatar samun nasara kuma ta zama alheri a Nijeriya" "Ban tunanin samun nakasu  a tafiyar nan a jihar nan, mun fito da hanyoyin fadakar da mutane kan alfanun tafiyar da yawa wasu sun yi danasanin zabar PDP a baya. Al'ummar Sakkwato in Allah ya ba da nasara za su samu tsaro da walwala za a yi duk abin da ya dace."

2023:Atiku Ne Yafi Cancanta A  Dukkan Masu Son Zama Shugaban Ƙasa-----Alhaji Auwalu Ila


Alhaji Auwalu Ila Wazirin Dundaye, PDP Emier a Nijeriya ya bayyana cewa yana  goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa  Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa ne saboda ya cancanta da kammala da sanayar da ya kamata mutum ya zama shugaban kasa,  'na tabbatar  duk abin da za mu yi   ya samu wannna nasarar za mu yi da ikon Allah.'
Alhaji Auwalu Ila a zanatwarsa da Managarciya a wannan satin ya ce Atiku yana da abubuwan da yafi dukkan 'yan takarar da ke son yin jayayya da shi, "ya yi zama mataimakin shugaban kasa shekara takwas ya san shugabancin kasa, dan kasuwa ne da ya san matsalar kasuwanci da 'yan kasuwa da hanyoyin magance matsalolin, don farfado da tattalin arzikin kasa, ya san aikin gwamnati don haka ya san yanda zai warware matsalolinsu, bayan zamansa dan siyasa kwararre wanda ya yi zama da Shehu Musa 'Yar'aduwa yakamata mu gayawa junanmu gaskiya shi ne kan gaba a cikin masu son PDP ta tsayar da su takara," in ji Wazirin Dundaye.
Ya juya kan maganar kin tsayar da Atiku ya ce 'bana ganin kadara za ta samu shugabannin PDP su yi  gangancin tsayar da wani ba Atiku ba, ganin jam'iyar tana tafiya ne kan  rokon Allah, abubuwa ana ganin haske a tafiyar da ake yi musamman kan tafiyar Atiku, tun sanda na samu damar cigaba da neman magoya bayan tafiyar Atiku ba safiyar da mutane ba su nemana kan tafiyar, in ka zauna wuri da mutum 10 Tara maganar Atiku suke yi muna fatar Allah ya sa ya zama mafita a Nijeriya.
"Maganar PDP ta yi shekara 16 tana mulki, a Arewa fa shekara biyu kawai ta yi tana mulki a cikinsu, hakan ya sa  muke fatan Arewa ta samu ta hannun Atiku don shi ne yafi cancanta," ya ja hankalin mutane. 
Mine ne alfanun Atiku yana fadin abin da yake son yi in ya samu mulki? ya ce  Amfanin fadin abin da yake son yi domin mutane su fahimta yin hakan cigaba ne gare shi da mu magoya bayansa yin maganar da yake yi ne ya sa mutane suka fahimci wane ne Atiku, bai samu nasara ba ne don haka Allah yakadaro ba don ba a gane yana da kwarewa ta mulki ba.
"Jam'iyar APC ta fada cikin rikici da bai da makama misali a jihar Kebbi tun 1999 ba ta taba fadawa rikicin siyasa kamar yanzu ba don rikicin ba a ma san ko ta'ina za a warware shi ba, yanzu haka sun kasa babban taronsu na kasa domin rikici ya mamaye su, a yanzu 'yan Nijeriya suna iya bambanta APC da PDP domin mu ba mu da rigima ko kadan."
Maganar goyon bayan Atiku ya aje Tambuwal ya ce "ita siyasa ra'ayi ce a gida guda ma za ka samu wani na PDP wani kuma yana APC balle maganar zaben dan takara, a 2019 Aminu Tambuwal  na goyi baya a Sakkwato yanzu kuma Atiku nake ra'ayi ina da hujjojina na yin haka, ina fatar samun nasara kuma ta zama alheri a Nijeriya"
"Ban tunanin samun nakasu  a tafiyar nan a jihar nan, mun fito da hanyoyin fadakar da mutane kan alfanun tafiyar da yawa wasu sun yi danasanin zabar PDP a baya. Al'ummar Sakkwato in Allah ya ba da nasara za su samu tsaro da walwala za a yi duk abin da ya dace."
"kashi 75 na abubuwan da nake yi kan matasa ne don su samu dogaro da kai da karatu yanda yakamata," a cewarsa.