Zaben 2023: Jam'iyyar APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabenta a jihar Yobe

Zaben 2023: Jam'iyyar APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabenta a jihar Yobe

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Yobe Alhaji Mohammed Gadaka ya amince da kaddamar da yan kwamitin yakin neman zabenta a jihar, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada domin tunkarar manyan zabukan shekarar 2023. 

 

Bayanin hakan ya na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai wadda Sakataren Jam’iyyar, Alhaji Abubakar S. Bakabe ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Damaturu.
 
Sakataren Jam'iyyar ya ce sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Yobe a zaben 2023 su ne Sanata Alhaji Ibrahim Geidam a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben, Sanata Ahmed Lawan, da Gwamna Hon. Mai Mala Buni a matsayin mataimakan shugaban kwamitin.
 
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Sanata Bukar Abba Ibrahim a matsayin Uba, sai Sanata Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar, Hon. Lawan Shettima Ali, mataimakin Darakta Janar a shiyya ta daya (Zone A) sai Farfesa Muhammad Bello Kawuwa, mataimakin Darakta Janar a shiyya ta biyu (Zone B) sai kuma Alhaji Muhammad Ismail Nguru, mataimakin Darakta Janar a shiyya ta uku (Zone C) yayin da Alhaji Barma Shettima zai rike Sakataren kwamitin. 
 
Alhaji Abubakar Bakabe ya kara da cewa, "Shugabannin jam’iyyar APC a jihar sun yi amfani da dogon tunani a tsanakee wajen zabo sunayen yan kwamitin yakin neman zaben, saboda irin kwarewa da jajircewarsu, tare da sadaukarwa da kuma kwarin gwiwa da suke dashi a kan yan kwamitin."
 
"Har wala yau kuma, jam’iyyar APC a jihar Yobe ta na da kwarin gwiwar cewa ‘ya’yan kwamitin yakin neman zaben zai kai jam’iyyar APC ga nasara a zabe mai zuwa. Kana kuma muna addu'a da fatan kwamitin yakin neman zaben zai gudanar da ayyukansa cikin himma da tsari." In ji Bakabe.