Tinubu Ya Dage Yakin Neman Zabensa  a Oyo Saboda Karancin Mai Da Naira

Tinubu Ya Dage Yakin Neman Zabensa  a Oyo Saboda Karancin Mai Da Naira
 
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dage gangamin kamfen dinta na shugaban kasa da aka shirya yi a jihar Oyo a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu. 
A wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, kakakin jam'iyyar a jihar Oyo, Olawale Sadare, ya ce an yanke shawarar jingine kamfen din ne saboda rikicin da ke kewaye da karancin naira da fetur, rahoton The Cable.
Ana ta zanga-zanga a yankunan kasar ciki harda jihar Oyo saboda karancin sabbin takardun naira da man fetur. 
Sai dai kuma, ana tsaka da ci gaban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a bashi dan lokaci kadan don daukar babban mataki kan karancin naira. 
Da yake magana kan dage gangamin, Sadare ya kara da cewar jam'iyyar za ta ba shugaban kasar lokaci don ya magance damuwar da aka shiga kan lamarin. 
"Muna bukatar ba shugaba Muhammadu Buhari damar yin aiki kan lamarin da kuma tabbatar da ganin cewa zaman lafiya ya dawo, musamman tunda ya shafi rikicin man fetur da takardun kudi. 
"A APC reshen Oyo, mun gamsu cewa akwai bukatar yin hakan don kada mu shiga hannun masu adawa da damokradiyya wadanda basa son ayi babban zabe mai zuwa. 
"Mun yi danasanin sanar da dage gangamin kamfen dinmu na shugaban kasa wanda aka shirya yi a ranar Talata har sai baba-ta-gani. 
"An dauki matakin ne duba ga matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu." 
Ya kuma ce jam'iyyar za ta sanar da jama'a sabon ranar da za ta yi kamfen din da zaran ta yanke shawara. 
Jam'iyyar ta bukaci masu biyayya gare ta da su kwantar da hankalinsu sannan ta nuna yakinin samun nasara a babban zaben, rahoton Arise News.