APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta A Watan Fabarairun 2022
Gwamnan Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya sanar da haka bayan sun kammala zama da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ofishinsa. Gwamnan na tare da rakiyar shugaban jam'iya na riƙo Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, taron gwamnonin APC da suka yi a ranar Lahadi aka cimma wannan matsayar da shugaba Biharo ya aminta da ita, a yi babban taro a watan Fabarairun 2022.
Jam'iyar APC za ta gudanar da babban taronta a watan Fabarairun sabuwar shekarar 2022.
Gwamnan Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya sanar da haka bayan sun kammala zama da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ofishinsa.
Gwamnan na tare da rakiyar shugaban jam'iya na riƙo Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, taron gwamnonin APC da suka yi a ranar Lahadi aka cimma wannan matsayar da shugaba Biharo ya aminta da ita, a yi babban taro a watan Fabarairun 2022.
Ba a sanya rana a watan ba sai bayan da shugaban jam'iya suka zauna za su fitar da jadawalin taron don sanar da hukumar zaɓe.
managarciya