Daga Ibrahim Salihu Isa Sokoto.
Bayan kwashe sama da shekarru Ashirin masu Lalurar gani na jagorancin hadaddiyar kungiyar masu Lalura ta musamman a jahar Sakkwato.
Ahalin yanzu dai an gudanarda zaben da dukkannin 'yan kungiyar masu lalura ta musamman a jahar sakkwato suka amince da shi bayan kwashe sama da Shekaru Shidda ana son yin zaben amma ya gagara saboda wasu dalilai na rashin fahimtar juna.
Alhaji Mu'azu Habibu wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar Guragu shi ne aka zaba azaman shugaban hadaddiyar Kungiyar masu Lalura ta kasa reshen jahar sakkwato, sai Sani Muhammad Dan'iya mataimakin shugaba na daya da Haliru Dahiru mataimakin shugaba na biyu da Mukhtar Sani Doki azaman sakatare shi kuma Nasiru Bunu mataimakin shugaba yayinda aka zabi Hafsatu Mu’azu shugabar Mata.
Sauran su ne Garba na Makka a matsayin ma’aji da Dahiru Ba'are sakataren kuddi da Mukhtar Gidan Igwai mai bincike yayinda Muhammad Rabo Binji ya samu mukamin jami’in hulda da jama’a.
Hakama kungiyar ta zabi Ibrahim Salihu Isa jami’in kungiyar na yankin Gabascin Sakkwato da Munirat M. Tukur jami’ar yankin tsakiyar sakkwato da kuma kabiru Bello jami’in kungiyar na kudancin sakkwato.
Acikin jawabin sa bayan kammala zaben sabon shugaban kungiyar masu lalura ta musamman a jahar sakkwato Alhaji Mu'azu Habibu yayi kira ga gwamnatin jahar sakkwato data cigaba da aikin inganta jindadin masu bukata ta musamman a jahar sakkwaton.
Alhaji Mu'azu Habibu yayi alwashin fitowa da sabbin tsare tsaren da zasu ciyar da kungiyar a gaba.
Da yake magantawa jim kadan bayan kammala zaben, wakilin ma’aikatar kyautata Walala da jin dadin jama’a na jahar Sakkwato, wanda kuma shi ne shugaban cibiyar horas da mutane masu lalura ta musamman Bilyaminu Muhammad ya godewa ilahirin mambobin kungiyar bisa ga irin kyakkyawan tsarinda sunkayi domin samun nasarar gudanarda zaben cikin ruwan sanyi.
Shi ma a nasa jawabin shugaban kungiyar mai barin gado Alhaji Haruna Muhammad Helele yayi kira ga 'ya'yan kungiyar da su bada goyon baya ga sabbin shugabannin kungiyar domin su samu nasara ga mulkin su.