Gwamnan Bauchi ya kori kwamishinoni biyar

Gwamnan Bauchi ya kori kwamishinoni biyar

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sake fasalin majalisar zartaswarsa tare da sallamar wasu kwamishinoni biyar.

A cewar wata sanarwa da mai baiwa Gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ga manema labarai a yau Talata, "wannan sauyin an yi shi ne domin inganta tsarin mulki da kuma tabbatar da ingancin gudanar da ayyuka ga al’ummar jihar."

Sanarwar ta bayyana cewa, “A bisa wannan mataki, an sallami kwamishinoni biyar. Wannan na nuna kudirin gwamnati na kawo sababbin tunani da kuzari cikin shugabanci, daidai da hangen nesan gwamnan na karfafa tsarin gwamnati da magance sabbin kalubale cikin nasara.”

Kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da Kwamishiniyar Ilimi, Jamila Dahiru; Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Abdulhameed Bununu; Kwamishinan yada Labarai da Sadarwa, Usman Danturaki; Kwamishinan Noma, Madugu Yalams; da Kwamishinan Harkokin Addini da Gyaran Zamantakewa, Yakubu Ibrahim.

Gwamna Bala ya mika godiyarsa ga kwamishinonin da aka sallama bisa sadaukarwa, hidima, da gudunmuwar da su ka bayar wajen ci gaban Jihar Bauchi.

Haka kuma, gwamnan ya mika sunayen wasu mutum biyar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin kwamishinoni da ga majalisar dokokin jihar.