2023:Wike Da Wasu Gwamnoni 5 Na Kokarin Ganin PDP Ba Ta  Tsayar  Da Atiku, Saraki, Da Tambuwal Takarar shugaban Kasa Ba

2023:Wike Da Wasu Gwamnoni 5 Na Kokarin Ganin PDP Ba Ta  Tsayar  Da Atiku, Saraki, Da Tambuwal Takarar shugaban Kasa Ba

 

Babban zaben 2023 na kara kusantowa gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike ya fito da makaman yakinsa a fili domin ganin ya hana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki da Gwaman Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal samun damar zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyarsu ta PDP.

Kamar yadda jaridar daily trust ta samu bayani Wike wanda kusan shi ne ke dauke da jam'iyar adawar a yanzu ya tuntubi  wasu takwarorinsa da wannan manufar.

Majiyar ta ce gwamnan yana son a baiwa dan yankin kudancin Nijeriya damar yin takara a 2023 a jam'iyarsu ta PDP.
Kamar yadda mutane ke tsammani gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad suna son jam'iyar ta tsayar da su takarar.
A gefe daya Atiku Abubakar da Bukola Saraki da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso nada bukatar yi wa jam'iyar takara.
Wata majiyar ta ce Wike ya ziyarci Bauchi da Adamawa da Sokoto da Abia da Enugu da Bayelsa da Oyo domin ya samu goyon bayan takwarorinsa gwamnoni, sai dai bayan wannan zagayen ya samu amincewa gwamnoni biyar kan manufar tasa.
Gwamnan Benue da Enugu da Oyo da Abia da Adamawa ne, a tafiyar ta su yanzu kenan  gwamnoni shida  ne kuma za su yi wahalar a kalubalance su ganin Wike ne ke dauke da jam'iyar, kamar yadda majiyar ta fadi.
Gwamnoni suna son a jingine dan takarar shugaban kasa daga Arewa a baiwa kudancin Nijeriya damar tsayawa takara a PDP.