GOSHI: Fita Ta Farko
GOSHI
*_MALLAKAR_*
*_Umma Yakubu Imam(Maman Dr)_*
P-1
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM!
"Baffa baka ba ni kuɗin makaranta ba kuma an ce duk wanda bai kawo sabon silifas ɗan-madina lamba arba'in ba ya zauna a gidansu ba sai ya niƙi garin zuwa makaranta ya yi wahalar banza da ta hofi ba, domin ko ya je sai ya sake dawowa gida. Cewar wata yarinya da ba za ta haura shekaru goma zuwa sha biyu a duniya ba. Baƙa ce wankan tarwaɗa, mai matsakaicin jiki da tsayi, idanuwanta da hancinta da bakinta daidai fuskarta. Mai yalwar gashin gira da na kai duba ga yadda yala-yalan gashin ke kwance luf akan saman goshinta da jagirarta kamar an dasa mata.
Sanye take da yinifom, mai launin bula da farin hijabi ta zubawa magidancin mutumin ido, wanda ta kira da sunan Baffa tana jiran harufan da za su feso daga cikin bakinsa. Baffa ya dubi yarinyar fuskarsa cike da mamaki fal ya ce"
"Silifas kuma uwata?
"I, silifas Baffa. Yarinyar ta yi saurin amsawa Baffa da jin haka ya sake cewa
"Ikon Allah! Su kuwa me za su yi da silifas ɗan-madina kuma lamba arba'in ba alli ko aizal ba? Na san dai su ake cewa ɗalibi ya kawo idan ya yi fashi ko ya yi lattin makaranta a cikinsu wane kika yi naga ba kya wasa da zuwa makarantar nan kullum Uwata? Kafin yarinyar da Baffa ya kira da uwa ta ta buɗe baki domin yin magana, sai da ta fara wasa da 'yan yatsun hannunta tukunna ta ce,
"Ko ɗaya Baffa, amma na ji malamin mu yana cewa zai je ƙauyensu to ina jin dai Kakarsa zai kaiwa tsarabar silifas din Baffa. "Don kawaii malaminku zai tafi ƙauyensu gaishe da kakarsa sai aka ce kune lallai za ku siyawa Kakar ta sa ɗan-madina lamba arba'in? Anya kuwa maganar ɗan-madina nan na da tushe uwata?
"Na rantse maka Baffa haka ya ce kuma wallahi duk ƙawayena sun kai ni kadai ce kawai na fita zakka a cikinsu ban kai ba Baffa ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimakeka a kasuwa ka saya min silifas ɗan-madina kar ƙawayena su yi mini dariya baffa.
Jimm! Baffa ya yi kafin ya ce" To ai shi ke nan. Tare da zura hannu a cikin aljihu ya zaro dubu guda, ya miƙawa yarinyar da ke baza murmushi tun san da ta ga Baffa ya yunƙura hannunsa cikin aljihu. Bayan Baffa ya miƙawa yarinyar dubu guda, tare da umarnin zuwa ta siyo silifas ɗan-madina ta kawo masa canji. Batare da ɓata lokaci ba yarinyar ta karɓa a guje ta yi waje, ba ta jima da fita ba ta dawo tare da silifas ɗan-madina da canji a hannu da ta miƙawa Baffa ya karɓa haɗe da zaro nera hamsin ya miƙawa yarinyar yana cewa"
Maza-maza ki wuce makaranta uwata kar ki yi latti, a yi karatu da kyau.
"To Baffa."
Yarinyar ta furta cikin murna, tare da juyawa a guje ta yo hanayar waje sai dai haɗuwar da jikinsu ya yi da wata matashiyar budurwa ya haddasa tsayuwar yarinya cak tare da jefowa matashiyar budurwar harara da ido, ita ma matashiyar budurwar cike da mamaki ta ce. "Ke wai dama har yanzu baki tafi makaranta ba da ? Uban me kika tsaya yi?
"Waya sani abu a duhu kuma bangaje ni da aka yi wuta-bal-bal ban yafe ba wallahi. Cewar yarinyar da ke sake hararar matashiyar, wadda kafin matashiyar ta yunƙura tuni yarinyar ta yi waje da gudu da silifas a hannu. Ƙwafa matashiyar ta ja kafin ta nufi cikin gida tana mitar idan yarinyar ta dawo za ta gaya mata wa ta yi wa wuta-bal-bal idan ita sa ar ta ce.
***
"Salamu Alaikuma. Inna Sahuwar ina kwana, an tashi lafiya?
"Wa'alaikis salam da GOSHI, d'iyar arziƙi irin albarka za a wuce makarantar ne yau ma?
"I, wallahi inna sahura da ma Baffa ne ya aiko ni na kawo miki wannan. Ta miƙawa dattijowar matar kafin ta cigaba da cewa, "Ya ma ce wai yana gaishe da Uwani Tifar yashi..."Kambura...ke don uwarki ban haramtawa ɗan iskan bakin ki kirana da Tifar yashi ba idan kika zo gidan nan?
"Assha! Assha!! Uwani rashin hankalinki ba zai taɓa haifar miki da ɗa mai ido ba, a ce mutum duk wata ƙofar alheri idan ta dirfafoshi sai ya yi ƙundumbala ya toshe ta don bala'i da nemarwa kai jarfa, to wallahi ki jini da kunen basira ba zan bari kwaɗo ya yi mana ƙafa a wannan karan ba maganaina sun gaji da yin tozali da kafaɗunki ga nawa dole ki san na yi ko kin ƙi ko kin so, to ma wai Uwani mene ne laifin yarinyar nan Goshi daga abin arziƙi sai ya zama na tsiya?
"To wai inna dole sai ta haɗa sunana da tifar yashi ne ni sa ar uwar ta ce ko ta ubanta da ba zata kira ni da sunan yanka na na Uwani ba, kwaran-kwatsa sai na zauneki na karya banza a banza na ga uban da ya isa ya tsaya miki a duk faɗin garin nan wallahi. "Ƙalu innalillahi wa inna ilaihirraju'una. Uwani na ce ba za ta kira ki da sunan yanka ba, shin Uwani tifar yashin ba sunan tsokanarki ba ne idan kin yi zuciya ki sace daga yau don Allah kar ki ƙara hawa kamar farashi an rasa me tayawa balle ya ɗauka.
"To wallahi Allah...
"Wallahi me? Kin ga Uwani idan baki rufe mini banzan bakinki a nan wajen ba zan ci ƙaniyarki wallahi, wake shin-shina takalminki duk faɗin garin nan idan ba uban yarinyar nan GOSHI ba? Sai ƙoƙarin faranta mini yake yi da abubuwan alkairi za ki yi min baƙinciki, ki kalli silifas ne ɗan-madina gal a leda da sabulu da omo har da gorona daushe mai ɗan karan daɗi.
"Ummm!!! Uwani ta furta kafin da bisani ta yi fuuuu za ta shige ɗaki ke nan yarinyar da ke durƙushe a gaban Inna sahura ta miƙe tsaye haɗe da buɗe baki ta ce"
"Uwani tifar yashi sai anjima...
Wani uban nishi da mulmulelen zagi Uwani ta feso daga cikin bakin ta kafin ta bi sahun yarinyar a guje da tuni ƙafarta ta tsallake soron gidan ta yi waje tana ɓalɓalawa uwani tifar yashi dariya har da gwalo, Inna na biye da Uwani tana kwara mata kira da ba ta san tana yi ba. Rashin kama yarinyar a hannu ya sa Uwani juyowa baya a zuciye tana buga tsaki tare da wallacewa sai ta gurguɗe bakin Goshi duk San da ta kamata koma me zai faru ya faru. Inna da ke yi wa Uwani sababi ta ce, "Kafin ki gurguɗe bakin yarinyar mutane ko sadaka ce na baiwa uban yarinyar ki je can ku ƙarata. Ba shiri Inna ta saɓi zani a jikin igiyar shanya ta yafa tare da fitowa daga cikin gidan.
....
"Gafaranku dai jama'ar gidan nan.
"A'aaaa, wa na yake gani kamar SAHURA? " Wallahi ni ce Adda Hauwa na tako da kaina ba saƙo ba. "Lale-lale, ga wuri ki zauna, bari in gyatta miki kayan nan. "Da kin bar su ma ai abin duk ɗaya ne.
Gaisawa tsofaffun biyu suka shiga yi da cigiyar yaushe gamo da junna duk da cewar ba nisa tsakanin gidajensu amma kamar sun shuɗe shekaru basu gamu ba. Inda Inna Sahura ta zayyanewa Adda Hauwa abin da ya kawo ta game da aiko Goshi ƴar ɗan ta da yake yi yana shinshina takalmin Uwani. Lamarin da ya tsunduma Adda Hauwa cikin murna da farinciki mara musaltuwa, domin Inna Sahura ta taɓo mata inda yake yi mata ƙyaiƙayi don ko kusa ba shiri take yi da mahaifiyar GOSHI ba, ta kuma amince da haɗin ɗari bisa ɗari ta ɗora da cewar ''Yau za ta aika a kira mahaifin Goshi ta ji daga gareshe a yi abin da wurwuri kar a baiwa ƴan baƙinciki ƙofar shigowa har su yi tsegumi.
Inna Sahura da Hauwa sun jima suna taɗi da tsara yadda za su shirya baki kafin Inna Sahura ta tafi cikin murna da farincikin karɓar Uwani da Adda Hauwa ta yi a matsayin sirika, wanda ya sa Adda Hauwa tashin Ɗan yayan mahaifin Goshi wato AWILO ya je gidan ya ce idan Baffa ya dawo daga kasuwa ya zo tana nemansa afujajan..
*******
Tun daga nesa yarinyar ta hangi tarin ƴan makara jibge abakin ƙofar shiga makaranta ana zane su ɗaya bayan ɗaya. Kamar yadda ta saba ƙin shiga ta cikin ƙofar makaranta haka yau ma ta yi saurin zagayawa baya. Ta cikin wani ginin makarantar da ya rushe ta sunkuya ta shiga tare da zagayawa wundon ajinsu tana leƙewa a hankali duba ga malama a ciki.
Lura da hankalin malamar kaco kam yana kan allon rubutu, cike da gwanancewa ta fara wurga jakarta ciki wadda ke kusa da wundon ta sakaye mata jakar cikin sauri. Nan take ta kama ƙarfen wundon tamkar biranya tare da tusa kai ciki ta zuro jiki a hankali tana shirin sauke ƙafarta ke nan malamar ajin ta jiyo jin ajin ya ɗau shiru tamkar mutuwa ta gifta....
@Real Maman Dr
(2025)
managarciya