INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya, Fita Ta Bakwai
To jiya naje zan wuce ta wajen mai gari sai naga wannan ta nuna wanda ta kwashe da mari, ya je gun mai garinmu yana gaya ma shi wai kuna nan kun shirya za ku shigo ƙauyen mu satar shanu da Awakai. Don haka abin bai min daɗi ba na zo don na gayama kasan dawa kake zaune ."
Page 7
Dabace wadda manyan ƙauraye da ƴan iska ke tattaruwa suka sheƙe ayarsu, ko da ta isa dabar sai wani tsamurarren saurayi ya dubeta yace, "Ke uwar me kika zo yi nan don mai garinku?
Hararanshi tayi ta wuce ya sake cewa, "Ke wai don Ubanki ba magana nake maki ba ?
Sai da ta ƙare masa kallo tas sai kawai ta kwashe shi da mari har sau biyu.
Nan da nan sauran mashayan suka iso inda suke suna ɗaga sanduna.
Kallon Barbushe tayi ta ce, "Duk da kai baka sanni ba, to ni na sanka domin duk inda kayi ina biye da kai birgeni kake don kallon Yayana Hafiz nake maka.
To jiya naje zan wuce ta wajen mai gari sai naga wannan ta nuna wanda ta kwashe da mari, ya je gun mai garinmu yana gaya ma shi wai kuna nan kun shirya za ku shigo ƙauyen mu satar shanu da Awakai. Don haka abin bai min daɗi ba na zo don na gayama kasan dawa kake zaune ."
Ai tuni wanda ta jama sharrin yayi wuƙi-wuƙi yana raba idanu domin shi dai bai san anyi ba, ga shi yasan halin Barbushe bai da mutunci yanzu ya farka cikin mutum.
Tuni idanun ƴan maza sun juye, ya kalli Lantai yace, "Yarinya ya sunanki ? Kin ce ni Yayanki ne ko ? Don haka kika zo kika gayamin yankan bayan da akai min ko?
Yana magana daddaga ƙatuwar addarshi ƙasa.
Duk da cewar Lantai ta tsorata sosai da yadda Barbushe ke caccaka wuƙar ƙasa yasa ƴan cikinta juyawa har wani zawo-zawo take ji.
Jira take kawai taga wani sabon abu ta kwasa da gudu.
Barbushe ba zato ba tsammani Barbushe ya zabga ma mashayin nan addar nan ya ja hannun Lantai suka shige gidansu.
Ta fara turjewa sai ta hango wata tsohuwa zaune tana gashin naman dawa ai sai ta gyara riƙon hannun Barbushe sosai lashe baki take kamar tsohuwar mayya.
Suna shiga tsohuwar ta ɗago kanta ta dubi Lantai ta ce, "Abin mamaki yau Isah kai ne tafe da yarinya kai da babu abin da ka tsana irin yara ?
Fuska murtuk ya zaunar da Lantai kan tabarma ya wuce ɗakinsa ya ɗauko mata ƙwaryar furarshi ya aje mata gabanta.
"Maza ki sha na kai ki gida kar dare yayi a zane ki gidanku duk wanda ya taɓa ki kuwa bai kwana lafiya na sha ruwan bala'i."
Ai sai Lantai ta tasa fura gaba ta fara sha , cikin ranta take cewa, "don Allah ji bi yadda wannan ƙaton mugun ke naɗar daɗi gidansu ? Ai kuwa kullum da nawa kason ba wanda zai min sagegeduwa nai asarar shagali.
Tunanin kuma kada ta cika cikinta da furar yasa ta aje ba don ta ƙoshi ba sai don kada naman can ya kasa samun wajen shiga.
Tsohuwar ta dubi Lantai "Yarinya ina ya samo ki kuma ? Ya sunanki ?
Lantai tai dariya ta ce "Sunana Nuratu amma dai Lantai ake kirana ."
Sai lokacin ya kalleta "Nuratu ai yafi daɗi ko a faɗa."
Tsohuwar na gamawa Barbushe ya ɗauko leda ya kwashi rabin naman ya zuba a ledar ya kama hannun Lantai yana cema tsohuwar "Inna bari na kai ƙanwata Nuratu gida na dawo."
Lantai ta dubi tsohuwar itama ta ce, "Innarmu sai anjima gobema zan dawo ."
Tsohuwa ta bita da adawo lafiya Lantai.
Suna zuwa daidai saitin da gidan Malam Muntasir yake Nuratu ta ce "Yayana kasan wancan gidan mai shi ya ƙwace min wani littafi kullum sai nayi kuka idan na tuna... Sai ta fashe da kuka kamar gaske.
Barbushe ya dubi gidan sosai yace "Ƙanwata daina kuka yau zan kawo maki littafinki idan kina soma sai na karya shi kafin na ɗauki littafin ."
Zawo ido tayi waje ta girgiza kai, "A'a Yayana kawai littafin nake so ni ka da ku taɓa shi littafin kawai nake so Yayana zaka ga littafin da hoton mace kamar matsafiya wata kala ."
Tsab tai masa kwatancen littafin domin tasan ba iya karatu yayi ba balle ta ce masa sunan littafin DORON MAGE .
Inna Kande tun bata damu ba har ta damu da rashin dawowar Lantai daga ta je ta samo mata goro yarinya shiru ?
Haka taita tunani har dai ta gaji ta saɓi gyalenta ta nufi makarantarsu Lantai taga ko tana can ta kasa samun goron ta kuma kasa tahowa gida?
Tana tafiya ta ci karo da Malamin kan hanya ta tambayeshi Lantai.
Malam Muntasir ya gaya mata hanyar daya ga Nuratu tayi .
Gida ta dawo tana ta tsogumin yawon Lantai yayi yawa idan Yayanta ya dawo zata sa yayi mata faɗan yawon.
Sallamar Lantai ta ji, da hanzari ta fito har tana tuntuɓe don ganin a wane yanayi Lantai ta dawo gidan?
Ganin Barbushe riƙe da hannun Lantai yasa Inna Kande fitsarin tsaye ta kama karanto addu'ar da duk ta zo bakinta.
"Yau ni Kande tsokanar taki akan wannan marar imanin ta faɗa yau Lantai ?
Inna Kande sai kyarma domin a gabanta kwanakin baya da akai faɗa da ƴan ƙauyensu Barbushe ya kwashe ma wani yaro hannu har zuwa yanzu hannu guda gare shi.
Inna Kande ganin kamar idan ya idaso inda take itama kwashe mata hannu zai sai ta koma ɗakin ta rufo tana cewa , "Yaro don Allah kayi haƙuri don Allah kada ka biye halin wannan ja'irar yarinyar wallahi marainiya ce amma bata ji sam."
Me Lantai zatai inba dariya ba? Ta dubi Barbushe ta ce "Yayana don Allah ka tsorata Inna Kande saboda kada ta bugeni don naje gunka ."
Ai kuwa Barbushe ya sake riƙe addarshi sosai ya nufi ɗakin da Inna Kande take yace, "Tsohuwa na rantse da Allah idan kika sake yau za a ci gumbarki ."
Inna Kande ta kama kuka tana cewa, "Kai ko yaro don Allah kai min aikin gafara na rantse da Allah ban san yadda Lantai tasanka bama .
Na shiga ukuna ni Kande yau kuma haka akai ?
Wayyo yaro kai haƙuri insha Allah ba zata sake ba."
Haka Inna Kande taita surutai tana ban haƙuri iri-iri .
Sai da Lantai ta tabbatar da Inna Kande ta gama tsurewa sannan ta ce, "Yawwa Yayana barta haka nasan ta razana."
A hankali Lantai ta kama kiran sunan Inna Kande tana cewa, "Inna Kande ki buɗe ƙofar ya tafi ai."
Sai da tayi magana sau kusan uku sannan Inna Kande ta samu da ƙyar ta buɗe ƙofar ɗakin.
Lantai ta kwashe da dariya ta nuna mata Barbushe dake tsaye riƙe da adda sai walƙiya take.
Ai da gudu Inna Kande ta sake yunƙurin rufe ƙofar Lantai ta tareta.
Shi kanshi Barbushe duk da bai dariya sai daya murmusa akan yadda tsohuwar taita rawar ƴan bori tana gaba tana baya .
Sai da Inna Kande ta jima kafin ta dawo hankalinta lokacin har Barbushe ya tafi da alƙawarin kawowa Lantai littafinta .
Inna Kande ta duni Lantai dake zaune kanta tana ta cin nama ta ce, "Ke yanzu Lantai gidan wa kika samo wannan mugun marar imanin ?
Lantai ta tuntsire da dariya ta ce, "Jikan naki ne mugu Inna Kande ? Inna Kande ta miƙe zaune tana tari ta ce, "Don Allah Lantai ki rufamin asiri kada ki jawo min tsohon bala'i da sabon bala'i duk su dira akanmu ."
Lantai dai sai cin namanta take tana kwasar dariya.
Inna Kande ta dubi naman ta dubi Lantai, "Kada ace saboda naman ya biyoki Lantai ?
Lantai ta yamutsa fuska ta ce, "Amma dai kin san ban sata ko Inna Kande ?
Ganin Inna Kande duk ta ruɗe yasa Lantai yi mata bayani kada ta kama zawo.
Da ƙyar Lantai ta samu Inna Kande ta ci naman saboda sai kyarma take har zuwa lokacin.
Barbushe na komawa ƙauyensu ya umarci yaransa da su shirya zuwa gidan Malam Muntasir don ɗauko littafin ƙanwarsa Nuratu.
Haka kuwa akai sai wajen takwas na dare suka bayyana gidan lokacin shi kuma malam Muntasir yana wajen mai shayi.
Gidan suka ɓalle kai tsaye suka shiga baki ɗaya suka zazzage ma shi duk kayan jakar da Lantai ta kwatanta ma Barbushe sai da ƙyar ya gane littafin suka fice batare da sun gyara komi ko sun ɗauki komi ba gidan.
Kai tsaye gidansu Lantai suka nufa daman batai barci ba tasan zai dawo tunda yace mata zai kawo mata littafin yau.
Inna Kande kuwa jininta kan akaifa yake domin ita dai bata amince da wai mutunci bane tsakanin Lantai da Barbushe sai dai idan zuwa yayi yaga abin da ke gidan ya dawo cikin dare ya yashe su.
Ilai kuwa taji tafiyar mutane cikin gidan kamar hada ƙarar wuƙaƙe ma, ai kuwa daga kwance ta sume inda take.
Lantai kuwa da gudu ta fice tana hango littafin a hannun Barbushe ta fasa ihu tana murna ta ruga ta amsa tana godiya suka juya suka tafi.
Me zai faru idan Malam Muntasir ya koma gidansa ya ga abin da akai masa ?
Yaya alaƙar Barbushe da Lantai zata cigaba ?
Inna Kande ya za tai ?
Haupha