ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 12
ANA BARIN HALAL..
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 12
Ina ajiye basket ɗin na sunkuya har ƙasa na gaishe su, bansan dalili ba sai na ji muryah na yana rawa, amsa mun gaisuwan sukayi amma ɗayan wanda naga kaman yafi tsayi kuma bai kai ɗaya jiki ba, lpy kawai yace ya maida kanshi kan wayan shi, ɗayan kuma wanda naga alaman yana ɗan jiki kuma yana da yawan fara'a, shi ya amsa mun fuskan shi kuma a sake, har ma ya tambaye ni suna, bayan na gaya mishi ya sake tambaya na s.s nawa nake? Nagaya mishi ina A.T.B.U zamu shiga level 2 next semester, zaro ido yayi cike da zolaya yace, "ashe mun kusa mu fara tara surukai, ni na ɗauka baki gama secondry school ba, wancan zuwan naga kaman ku biyu ne kan ku ɗaya ko"? Ɗaga kaina nayi alaman haka ne, "tou ina ɗayar? Don naji Ahmad na ƙiranku twins, hakane?" nan ma murmushi nayi na sake ɗaga kaina alaman haka ne, dariya yayi mai ɗan sauti yace, "inaga kema irin yayan kine, magana yana baku wahala", "kai kuma babu abu mai sauƙi a wurinka irin magana" naji ɗayan farin ya faɗa, da sauri na ɗago ido na kalle shi, abun mamaki ko kallon mu baiyi ba yayi maganan, daga gefe kuwa yayah Ahmad yana murmushi yace, " Ayshaa idan kin shiga kicewa ummi su A.G zasu shigo su gaisheta idan mun gama", miƙewa nayi da sauri ina amsawa yayah da tou, shi kuma ɗaya mai yawan fara'an naji yana faɗin "haba Barrister muna ɗan labari kuma ka sallameta? Bayan nasan dukkan ku yanzu kowa zai rungumi waya yayi ta faman danne-danne ku bar ni shiru", "tashi kije ciki ki isar da saƙon ki, ki rabu da yayanki mai yawan maganan nan," naji muryan ɗayan farin ya faɗa, da sauri na ɗago dara-daran ido na nadube shi, cikin sa'a kuma shima idon shi na kaina, rikicewa naso yi wanda bansan dalili ba, da sauri nayi hanyan waje.
Wajajen shaɗaya da rabi naji muryan su yayah da abokanshi a parlon ummie suna gaisheta, haka nakasa kunne nake sauraron gaisuwan su, inda naji yayah yana ambatan A.G da kuma M.G, ƙasa-ƙasa nake jin muryan ɗayan wanda bansan ko shine A.G ɗin ko M.G ɗin ba yana mata godiyan masan da aka kai musu, daga baya naji muryan ɗaya mai yawan fara'an shima yana godiya, zasu fita naji muryan shi yana tambayan hafsy ni, sokuwa naji tana cewa kaman bacci nakeyi, naji kaman na garzayo da gudu nace gani, amma sai na daure na gayara kwanciya na, a zuciya nace maganin mai baccin ƙarya, ɗazu ina ji hafsy na ƙirana nayi likimo, basu fi minti biyar da fita ba naji muryan Yayah Ahmed a parlon, da sauri na dirƙo a gadon nayi parlon, fuskana a murtaƙe na nemi wuri kusa da shi na zauna, idon shi akaina yace, "fatan kina lafiya dai ko"? Ɗaga kai nayi alaman eh, "yau kina azumin magana ne? Har kin sa M.G ɗazu yana cewa halin mu ɗaya, saboda shi Allah yayi shi mai son hira, baya so yaji an zauna shiru, da badan A.G ya sallameki ba haka zai ta cika mutane da surutu", ya ƙarasa faɗa yana dariya, nima murmushi nayi nace, "su ɗin ƴan gida ɗaya ne yayah"?
"maƙota ne kawai, amma sun dawo ƴan'uwan juna, kuma sai akayi dace sunan iyayen su yazo ɗaya",
Ummi tace "gashi ni har kama ma suke mun, yanzu dama maƙwafta ne ba ƴangida ɗaya ba? Kasan kullum da kake bani labarin su tun kafin na gansu na ɗauka ƴan gida ɗaya ne", murmushi yayi yana ɗaukan ruwan da hafsy ta ajiye musu yana buɗe bottle ɗin, "wallahi ummi nima farkon haɗuwa na dasu na ɗauka ƴangida ɗaya ne, irin kowa da maman shin nan, kinsan a school of low muka haɗu da shi A.G ɗin, ummi bamu mintuna kaɗan zakiji ƙiran M.G ɗin yana tambayan lafiyan A.G ɗin, kin san A.G ɗin yana da athsmah, kuma lokacin kaman ya ɗan matsa mishi, duk hankalin M.G ɗin a tashe, daga baya A.G ɗin ya gaya mishi ya haɗu da wani ɗan bauchi kuma yana taimaka mishi wato ni, haka M.G ya matsa ya karɓi wayana, ƙira akai akai yaji yyh A.G yake, na ɗauka nima yayan shi ne, ashe maƙwaftah ne suka taso tare, don kinga M.G a gidan su A.G ma yake zama ɗakin shi a gidan shima aka mishi saboda abotakan su ya dawo....." bai ƙarasa ba muakji sallaman yayah umar, haushi naji na ɗan harare shi saboda ya yanke labarin da yayah Ahmad yake bamu don so nakeyi naji ƙarshen labarin, kuma sanin halin yayah Ahmed dama maganan ba damun shi tayi ba, irin haka kawai kake ɗan jin maganan shi, hakan ma sai idan akwai ummie ko Abbah ko yayah mohd a wurin, da gudu hafsy tayi wurin shi ta rungume shi tana mishi oyoyooo, dama ta hannun daman shi ne, hararah na yayi dole na tashi naje mishi oyoyoooo amma ya matsa gefe yana gwale ni, "sai da kika dama tukun kika wani kwaso tsumman ƙafan ki ko"? Tou bana so koma chan da munanan idon ki a wurin da ƙaton kai" dariya mai ɗan sauti hafsy tayi saboda daɗin an kushe ni, tsayawa nayi kaman zan mishi kuka baki na a zunɓure, juyawa nayi na kalli yayah Ahmad nace "ka ganshi ko yayah" Rungume ni naji yayi yana dariya yana faɗin "wane ni na gwale ki wanda tafi kowa kusa dani a duniya, kin san fah da tare ummie zata haife mu ke kuma Allah yayi ki mai sanyin jiki, shiyasa na fole ki da ƙafa kikayi baya na iso duniyan, tsabar sakarci da son jiki sai da kika ɗauki tsawon shekaru kina jinya kafin kika zo duniyan", ya faɗa yana dariya, gaba ɗaya su ummie ma dariyan sukeyi, sannan ya ƙarasa wurin yayah Ahmad ya ɗan sunkuya ya rungume shi yana yayah na rabin jiki na, yayah Ahmad yana murmushi yace, "kun iso lpy corpers?" yayah umar yana dariya yace, "yaya munyi passing out mun dawo kenan", ya faɗa yana wucewa wurin Ummie itama sunkuyawa yayi ya kwanta akan cinyanta yana, "Ummie na my first love na dawo na sameki lafiya cikin kwanciyar hankali, raina yayi daɗi" ya faɗa kaman yana wani ƙara rungumeta, domin gaskiya yayah umar shi yana da maƙon iyaye da ƴan'uwa, don zan iya ce miki duk cikin mu yafi irin nuna damuwa da nashi, shidai barshi da masifa da zafin zuciyan shi, amma yana nuna ma kowa so.
Hafsy ne ta shiga kitchen ta haɗo mishi masa da kunun gyaɗan da ummie tayi, dama ummie ita bata abinci kaɗan takanyi wanda ko baƙo akayi babu batun jin kunya, babu daɗewa mamah ta shigo daidai nan yayah mohd ma ya shigo, haba gaba ɗaya sai aka kachema da hira, kowa kaman zai cinye ɗan'uwan shi don so, irin waƴan nan lokacin idan muka haɗu sai dai kaga ummie fuskanta kaman gonan auduga, ta juya kan wannan ta juya kan wannan, "Allah sarki ummin mu, gaskiya *Aunty nice* Allah yayi mana kyauta mai daraja da ya bamu ummie a matsayin uwa, macece mai tsoron Allah, Allah sarki ummin mu".
Sun kuyar da kai Hajiya Ayshaa tayi ƙasa tana share hawayen da ya biyo kan kyakkyawar fuskanta,nidai sai naji duk jikina yayi sanyi, na tsura mata ido a zuciyana nace, Allah yasa dai ummin nata na da rai, don ni nasan zafin mutuwar iyaye, uwa ko uba duk wanda ka rasa sai kaji kaman baka da sauran komai a cikin duniya.
Ɗagowa tayi ta dubeni tana share hawayen ta, amma fuskanta cike da murmushi, nima murmushi na mayar mata, bayan ta gama goge fuskan ta ta ɗago ta kalle ni sannan ta cigaba da bani labarin ta.
A irin wannan lokacin mamah takan zauna a side ɗin ummie, abun da na lura daɗi takeji idan ta ganmu dukkan mu a hallare, kuma sai kiga kowa a cikin mu yana nan-nan da ita, domin babu laifi mamah tana da zuciya mai kyau, kuma idan za'a wuni itama ranan ko abinci bata ɗaurawa anan take zama, saidai idan itace da girki zata tashi zuwa wani lokacin, sallan azahar da akayi ma zuwa sukayi sukayi sallan sannan suka dawo nan parlor, basu suka bar gidan ba sai bayan la'asar lokacin kowa yaci abinci sannan suka watse, ana sallan ishaa sai ga yayah umar da yayah ishaq aminin shi sun shigo, bayan sun gaida ummie basu wani zauna ba suka wuce chan side ɗin aminiyar su hajiya ummah, nan kuma hafsy ta bisu, domin na hannun damanta yayah ishaq yazo.
Washegari haka nayita kasa kunne naji yayah Ahmad yayi maganan su A.G amma shiru, nayita zura ido ko zanga sunzo, amma shiru babu ko gilmawar motan su, haka da yammah na wuce gidan su maryam, ina shiga ta taso da ihu ta rungume ni, maryam duk duniya idan kika cire habiba tou babu wanda yasan sirri na kuma nake iya gaya mata komai a rayuwata sai ita, ita jamilah abun da na lura wani irin so na Allah ya saka mata a zuciyarta, don gaskiya sun zaune sit ɗaya ne da habiba, amma don ta ita bataƙi dani take tare ba, don ni komai nayi dai-dai ne a wurinta, don har tsokanan ta sukeyi wataran wai mayyar Ayshaa, kuma bata gajjiya da kallo na, idan na kamata tana kallo na sai tayi murmushi tace, "Ayshaa duk duniya babu mai irin kyaunki, don ni da madkhuri kike mun kama, kyaunki yana da kyau sosai", nidai murmushi kawai nakeyi idan ta faɗa, lokacin zakiga habiba da maryam sun hayayyaƙo mata, ita maryam abunda na lura ita kuma son da take mun bata so taga wani yana mun irin wannan son, don kullum cewa takeyi Ayshaa nata ne, ita kawai kishina takeyi don ko habiba ne ta cika shige mun haushi maryam takeji, ita ko tafiya akeyi tafi so ta tsaya ta gefe ne, gaskiya *Aunty nice* bana gane wacece tafi sona a cikin maryam da jamila, amma nidai har ga Allah nafi son maryam, mun taso tare kuma muma maƙwaftaka, gashi ni ganinta nakeyi kaman ƴar gidan mu ita, ɗakin maryam muka wuce muka zauna, hannu nasaka nayi tagumi na zura mata ido, dariya ta kwashe da shi tace, "duk wannan tagumin na rashin jin ƙarshen su farare ne?" tsaki naja nace, "matsalata da ke idan ana magana mai muhimmanci ke ba'a nan kike ba", dariya ta sheƙe da shi tace, "tou ke yanzu wannene naki?"
Hararanta nayi nace "nawa kuma? Son su ma kenan nakeyi? Bakiji nace miki ni kawai kyau suka mun ba, amma yayah ma za'ayi ina mace na so su"?
Dariya maryam ta kwashe da shi da shi tace, "sokuwa tou ni nace miki son su kikeyii? Kawai dole akwai wanda yafi burge ki a cikin su shine nufi nah",
Ajiyan zuciya na sauƙe mai girman gaske nace "ni duk burgeni sukeyi, don dukkan su farare ne, kuma kyaunsu duka mai kyau ne, amma ɗaya baida magana ɗaya kuma yana da magana, kuma fara'ar fuskan shi tana burgeni", na faɗa idona akanta, shewa tayi tace tanaga mai fara'an ne zai zamu na hannun dama na, saboda ni shiru shi magana, abun zaifi, don idan na haɗu da mai shiru irina abun ba zaiyi armashi ba,
"me kike nufi ne maryam? Kina ɗauka ni ina son su ne?"
Kama baki tayi tace, "na isa nace ke kina son su? Ae babu so a wannan al'amarin kawai burgewa ne, nima har naji ina son ganin su, suna zuwa ki zabga mun ƙira", ta faɗa tana wani dariyar shaƙiyan ci, nidai tsaki nayi na miƙe don tafiya gida.
*AUNTY NICE*
managarciya