ANA BARIN HALAL.:Fita Ta Uku

ANA BARIN HALAL.:Fita Ta Uku

ANA BARIN HALAL.:


*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*


*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*

*PAGE* 3


Duk yadda mamie ta kai da son ta raba tsakanin ƙawancen mu da Habibah abin ya gagara, don rana ɗaɗɗayane bata shigowa side ɗinmu tayi masifa wa Ummi, akan dole idan mun shigo Ummi ta kora Habiba, sbd ni babu yadda za'ayi naje side ɗinsu sai mamie ta kore ni, har nadawo ma bana son zuwa, saidai ita Habibah tazo wurina, amma ko sau ɗaya Ummi bata kula ta, watarana ne ma Yaya Umar yazo suna zaune da Yayah ishaq a parlon mu sai ga Mamie cikin bala'inta ta shigo neman Habibah, inda ta shiga batanan ta ke fita ba, gashi bata san Yayah Umar yana ciki ba.


Ranan na tabbatar Yayah Umar gwarzo ne, don tsabar masifah da ƙyar Hajiya Ummah ta shigo da Mamah suka fitar da shi, don rantsuwa yayi akan idan Mamie ta sake shigowa tayi rashin kunya wa Ummin mu ko ta nemi shiga tsakanina da Habiba wlh sai ya mata dokan tsiya, jikin shi har wani rawa yakeyi kaman wani ɗan gunda.

Ita dai mamie jiki a sanyaye taja tsumman ƙafarta ta juya tayi side ɗinta, ƙasa-ƙasa ta ke magana akan yajira dawowan  Abban mu, wlh bazata yadda ba, aiko batayi nisa ba, ya biyo bayanta idon shi kaman zasu zazzago yana zare su yace, "wlh ummi na rantse miki da Allah idan baki gayawa Abba baki cika mai sharri ba, kuma ni da kaina zan gaya mishi, ya kuma ja miki kunne akan zuwa gefen mahaifiyata, don wlh idan kowa bai ɗauki mataki ba ni nan".... Yana buga ƙirjin shi da hannu yana nuna kanshi yace "zan ɗauki mataki mai tsauri akan ki da shegiyar munafukar ƴar ki mai kai miki rahoto".. Ya juya da sauri yana neman Raliya.

Ganin haka Ummie ta ƙaeaso wurin ta kama shi, "Umar na baka umurnin ka fita kada ka taɓa yarinyar nan," daga nan ta haɗa hannun shi da Ishaq tace sufita zuwa wurin Hajiya Ummah su zauna, bata son fitina.

Tsaki Mamah taja tana hararan Ummie tace, "amman ummin su ke ina ruwanki ne? Ki bar shi ya chasa mana munafukar yarinyar nan mana, itama uwar munafukan ae shine daidai ita", tana gama faɗa ta juya ta tafi side ɗinta, aka barni nida Habiba muna tsilli-tsilli da idanu, don Allah yana gani muna son junan mu sosai, kuma kullum Abban mu yana nuna muna musu junan mu, yana jin daɗin yadda muke tafiyar da rayuwar mu, haka ma Ummie da Yayah mohd, gashi ko sch class ɗin mu ɗaya  sit ɗinmu ma yana bayan nasu Habibah.

Maƙwaftan mu muna da wata ƙawar mu mai suna Maryam, maryam itace sit ɗin mu ɗaya da ita, ita kuma Habiba suna zaune da wata friend ɗinmu Jamilah, ita jamila a fadamar mada suke, maryam kuma unguwar mu ɗaya da ita, wato G.R.A, gida ɗaya ne tsakanin mu da su, kuma tun shigan mu primary class ɗinmu ɗaya sit ɗinmu ɗaya, har zuwa yanzu da muke shirin rubuta junior weac.

Ana gama watsewa a wurin muka haɗa ido da Habiba, kaman wasu dolaye muka kwashe da dariya, Habiba ta matso kusa dani tana zare ido tace, "sis yau kam zanci na jaki a wurin Ummie babu mai karɓa na, yau kam jikina zaiyi yakuwa", tana gama faɗa muka sake kwashewa da dariya, nima cikin zare ido na sunkuya dai-dai fuskar ta, don nafita tsayi sosai, Habiba guntuwa ce kaman Mamanta, ni kuma daga Abba har Ummie dogaye ne, sai yazama gaba ɗaya ɗakin mu muna da tsayi, kuma dukkanmu farare ne sol, su kuma kasancewar maman su guntuwa ne sai Habibah ta ɗauko guntancin maman ta, amma farin Abba ta ɗauko, sbd haka banbancin mu babu yawa a haske, don ita har taso ta fini, don ni na sirka da ɗan jaja haka, amma Raliya baƙa ce, ta ɗauko kalan fatar Mamie da kamannin mamie, sai dai ita doguwa ce, don tsayin su ɗaya da hafsy, "Sis kawai mu gudu wurin hajiya ummah, har sai Abba yadawo munga abun da hali yayi, idan ba haka ba ina tsorata miki na jaki da zaki sha yau", na faɗa ina kama hannun ta mukayi wurin kakarmu.


Ana daf za'ayi sallan magrib Abba ya dawo daga tafiyan da yayi zuwa Abuja, ta window muka leƙo nida Habibah muna ganin masu aiki dasu hafsy da suke masa sannu da dawowa, inda ya rungume hafsy da Raliya a jikin shi, Abba yana son mu, wani irin son da ko iyayen mu mata basa nuna mana, da gudu muka fito mukayi wurin shi, fuskar shi cike da fara'a yana, "oyoyo ƴan biyu na," mukaje ya rungume mu, muma muna mishi oyoyo Abba, Yayan Ahmed ne ya fito a motan shima fuskar shi cike da farin ciki yana kallon mu, hannun shi riƙe da hannun hafsy da raliya, don tare suka dawo da Abba, farin ciki kaman zanyi yaya ganin an fito da kwakwa daga boot ɗin Abba, ina kallon Habiba nace, "sis gobe akwai kwakumeti a gidan nan", Abba ma yana dariya yace, "ae saboda ku na ce dole a sayo kwakwa a gidan nan, ƴan biyu na zasu mun kwakumeti naci,"

"Abba mu kuma fah"? Cewar raliya da ta zunɓuru baki gaba, tana sake hannun yayah Ahmed ta taho wurin Abba, "ku kan ae baku da tsaraba sbd yawan masifar ku da faɗan ku, shiyasa ma ku bana ganin ku kaman ƴan biyu," Abba ya faɗa yana wuce side ɗin Hajiya Ummah, sannan yacewa Yayah Ahmed yayi alwala bari yagaida jatumar sa sai su wuce masallaci.


Yayah mohd da Yayah Ahmed basu da hayaniya, amma na Yayah Ahmed har ya ɓaci, sbd shi komai kukeyi baya tankawa, maganar ma da ƙyar yake iya buɗe baki yakeyi, don kullum ina jin Ummie tana cewa yayah yake iya magana a kotu?
Wucewar Abba kaɗan raliya ta juyo ta zabga mana harara, sannan taja tsaki tace, "wallahi duk iya munafurcin ku kwakwan nan namu ne mu duka, tare za'ayi kwakumetin, ko kuma kunayi na faɗawa Ummie ta ƙwace ta  raba mana dai-dai wa dai-dai, kunga ku da shan wahala mu kuma da morewa"' ta faɗa tana murguɗa mana baki kaman sa'o'inta.


Mari hafsy ta kai mata a bakinta tana, "mumafuka mai zubin shaiɗanu, shiyasa kikayi baƙi ke kaɗai a gidan nan sbd baƙin zuciyar ki"  aiko raliya ta juyo zasu kama dambe da masifar su, Yayah Umar ya daka musu tsawa wanda lokacin fitowar shi kenan daga side ɗinsu, marasa kunyan banza da gudu sukayi cikin gida, amma bakin Raliya bai rufa ba tana cewa, "wallahi sai na haɗaki da ummie, kince a wurinta na ɗauko baƙi da baƙin hali", mudai kallon mamaki kawai muke musu nida habibah.


Kama hannu mukayi muka wucce side ɗin hajiya ummah, dai dai lokacin kuma yayah umar suna gaisawa da yaya Ahmed, hannun su riƙe da na juna, sbd gaskiya yayuna ukun nan akwai ƙauna mai girma a tsakanin su, idan ka gansu kaman abokaina, muma wucewa mukayi side ɗin Hajiya Ummah inda muka haɗu da Abban mu yana shirin fitowa.


Bayan anyi sallan ishaa an haɗu a dinning wurin cin abinci, ido na nida Habiba zuru-zuru muna jiran ko mamie zatayi wani magana akan faɗan ɗazu amma shiru bata ce komai ba, sai dai hararan mu da takeyi a kaikace nida Habiba.


Ana gama cin abinci Yayah Umar ya dubi Abban mu da ke shirin tashi ya wuce cikin parlon yace, "Abba ina son magana da kai" da ɗaurarren fuskan shi kaman shine maigidan ba yaron gida ba, da sauri Mamie ta ɗago tana duban shi, ita kuwa Ummi baki ta buɗe tana, "Ubanah bana son dogon magana fah" babu ɓata lokaci Abba ya ɗaga mata hannu, da nufin ta mishi shiru, yana bada hankalin shi gaba ɗaya kan Yayah Umar.

Girgiza kai Mamah tayi irin alaman Abba ya mata dai-dai, tana hararan Ummie.

"Abba dama alfarma nake nema a wurinka, ina so kayiwa mamie magana akan duk wani abu a gidan nan da ya faro ko akan yara ko na cikin gidan nan, kada ta sake zuwa kan ummie da faɗa, idan ba haka ba wlh Abba wataran labarin da za'aji bazaiyi daɗi ba, don gsky ni haƙurina yana gazawa," ya faɗa yana hararan Raliya ƙasa-ƙasa.


Kaman Abbah bazaice komai ba, har zuwa wani lokaci idon shi yana kan Yayah Umar, zuwa wani lokaci kuma ya maida kan ita mamin, gyaran muryah yayi sannan yace, "Baba nah kafin kagaya mun kai Ummah ta gaya mun, kuma insha Allahu zamu zauna da iyayenkan, kuma zanyi maganin komai, zan kuma kawo ƙarshen komai insha Allahu, kaima ina son ka dinga haƙuri da wani abun, kana kuma kawar da kanka akan su", da sauri mamah ta buɗe baki cikin ɓacin rai tace, " sai an kai uwarshi ƙasa tukun zaiyi magana? Wannan ae ba shari'a bane, shiyasa kullum Hauwa takeji a ranta abun da takeyi dai-dai ne, don ba tsawatar mata akeyi ba" ta faɗa tana miƙewa tsaye da niyyan barin wurin, Abba ya dakatar da ita, "Zainab bawai bana lura da abinda yake faruwa bane ko bazan ɗauki wani mataki akai bane, nan ae ku da yaranku ne zaune, kuma naji ƙorafin Baba na, insha Allahu zan zauna daku muyi magana, ba lallai sai a gaban su ba", ya faɗa yana mai da kallon shi kan mamie da ta wani tura baki gaba kaman zata zunduma ashar, sai dai babu dama, don daga Mamah har Yayah umar tana shakkan su, haka kowa ya tashi yayi side ɗin shi, amma Yayah mohd, yayah Ahmad, Yayah Umar, Hafsy duk miƙewa sukayi suka wuce side ɗin Ummin mu, mu kuma ganin Abba zai tashi da wurin mukayi hanyar Hajiya Ummah, don gaskiya yau babu mafaka a wurin Habiba sai chan, munafukar kuma Raliya muna shirin fita tana hararan mu, mudai bamuyi takanta ba muka wuce.


Hajiya Ummah tana ganinmu ta harare mu, cikin hararan mu tace, "nice rumfah sha shirginku ko? Idan ana zaman Allah da annabi ne ina binku kuzo mu kwana sai kuƙi, ku masu iyaye sai ku gudu chan, idan sun gallabe ku kuma sai ku kwaso mun ƙazamin jikinku kuzo ku takurani ni da gidan ɗana," ta faɗa tana maida kanta da hankalinta kan T.V, dariya muke mata Habiba ta faɗa jikinta tana dariya, ni kuma na zauna wurin ƙafanta ina nawa dariyan, Habiba tana neman tsokano mana ita tace, " hajiyar mu maganin kukanmu, idan bamu zo wurinki ba wurin wa zamuje? Kinyi na Abban mu kina namu, ae kin muri duniya da abunda yake cikin duniyan, ƴaƴanki su miki jikoki su miki", nima ina dariya na chabke da "gashi muna haihuwa ƴaƴanmu na fari masu sunanta zamu saka".


Buɗe baki tayi tana kallon mu cikin mamaki tace, "amma Allah yayi manyan maƙaryata a nan, ae idan na samu kuka cigaba da zumunci dani ma ae nayi sa'a, da shegen bakin ƙaryanku ae kuna haihuwa kowa wa uwarta zatayi wa mai suna, babu ma ya waƴennan gardawan Umar da Ishaq, duk sun lotsa mun gado da kujeru na, amma nasan sunayin na kansu bazasu taimakeni ba, ballantana mai suna, sai gatan kashe mun kujeru da yawan zamansu" ta faɗa fuskanta a murtuƙe, dukkan mu dariya muka kwashe da shi, habiba tana ƙara ingiza magana da cewa tun ba ma Yayah Umar ba, don naga ya sakoki a gaba da labcecen jikin shi, juyawan da zanyi kawai sai na ganshi a tsaye a bakin ƙofan parlon, ae banbi takan Habiba ba na rantama ɗakin Hajiya ummah da gudu na murɗa key, ina jin dariyar Hajiya Ummah don babu abinda takeso irin taga yayah umar yana labtan mu, ina jingine da ƙofan ina dariyar Habiba ko ita ina tayi, don naji ihun ta da gudun ta.

*AUNTY NICE*