Gwanar Mata Da Kananan Yara--- Dakta Larai Aliyu Tambuwal

“A matsayina na ‘yar jihar Sakkwato ina jin takaicin  zaman banza da lalaci da maula, haka ma ina bakin ciki duk lokacin da naga  ana zalunci da rashin gaskiya don samun nasarar rayuwa. Ina tsananin kishin jiha ta; ta zamo kan gaba a kowane fanni na rayuwa. Maza matasa da mata su jajirce su zama masu cin gashin kansu ba ci-ma kwance ba, ina mai kwadayin ganin ‘ya’yan Sakkwato sun bayyana a kowane mataki na cigaba a gida da waje don kawar da maula da tumasanci.” “Ina matukar tausayin talakawa da masu karamin karfi idan sun shiga halin matsi ko kaka nika-yi, in da hali bana ganin hasarar taimakawa da ba da tallafi daidai gwargwadon hali na, ganin yanda nake diyar talakawa na samu tallafi na tsayu da kafafuna, haka nake son sauran jama’a su samu su kafu,  da irin wannna damar su kaucewa kalubalen rayuwa wanda zai iya gurgunta su.” A cewar Dakta Larai baya goya marayu.

Gwanar Mata Da Kananan  Yara--- Dakta Larai Aliyu Tambuwal
Dr. Larai Aliyu Tambuwal

 

“Ina fatar ganin mata na jajircewa a kowane fanni na cigaban rayuwa, haka kuma marasa galihu da masu karamin karfi na samun kulawa gwargwadon abin da rayuwa za tabukata don ta inganta.”

 

 

Dakta Larai Aliyu Tambuwal hazika ce da son cigaban al’umma wadda ta bar abin koyi a rayuwarta ga duk wata mace mai son kawo cigaban jama’a don a gudu tare a tsira tare. A zantawarta da Managarciya  ta fito da bayyanan rayuwarta sosai da za su kara zama madubi a halin taimakon al’umma da take yi.

An haife Dakta Larai  a garin Tambuwal ta jihar Sakkwato ranar 16 ga watan Satumba 1971, ta tashi a hannun kakanninta  duk da cewa mahaifanta dukan su ‘yan garin Tambuwal ne.

Ta yi karatun Alkur’ani a hannun Malam Ahmadun Jega a zawiyyar  Tambuwal, haka kuma ta yi karatun firamare a (Town Primary Tambuwal) wadda ta koma Buhari Model  a 1978 zuwa 1984.  “Na fara karatuna na sikandare a  makarantar mata ta Nana a birnin Sakkwato 1984 zuwa  86 amma na kammala a makaratar mata ta gwamnati(GGC 1986-1990).” A cewar Dakta Larai.

A lokacin tana  sikandare rayuwa nada dadi da sauki, ta rike mukamin shugabar aji(class monitor) da shugabar daliban makarata (Head Girl) a lokacin tana da sha’awar wasanni ta halarci ‘extra  curricular activities’ da dama kamar ‘Schools debate  competition, quiz,   cultural displays, girls grid,  mamser brigade, WAI brigade,’  da wasannin motsa jiki kamar volley ball, hokey, racing competitions’. Wannan ya ba ta dammar samun horo na kwarai da ya shirya ta  shiga gwagwarmayar rayuwa.

Bayan ta kammala sikandare ta fara karatun share fagen shiga jami’a  a ‘school of basic studies Samaru’ a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya na tsawon wata shida, daga nan sai jihar Sakkwato ta ba ta tallafin   karatu na samu gurbi ta je kasar Bulgariya ta yi karatun likitanci a wata jami’a da ake kira(Higher Medical University) a garin Ploudiv a kasar a 1992 zuwa 2000.

Bayan dawowa daga karatun likitanci ta kama aiki a asibitin mata da kananan yara ta Maryam Abacha tsakanin shekarar 2000 zuwa 2006 a haka ta yi jarabawa ta  hukumar kula da likitoci ta Nijeriya(Medical and Dental Council of Nigeria) a jihar Legas da Zariya, don in yi rijista da samun lasisin yin aiki a Nijeriya a matsayin likitan jama’a. Haka kuma ta yi aikin ‘Housemanship’ a asibitin koyarwa ta Usmann Danfodiyo a 2001 zuwa 2002, da aikin bautar kasa NYSC a asibitin Maryam Abacha a Sakkwato.

“A shekarar ta 2006 na sake komawa jami’ar Usman Danfodiyo a inda na kamala digiri na biyu (Master of Public Health 2006-2009). A saboda haka ne Gwamnatin Sakkwato ta sake bani tallafin karatu don yin karatun kwarewa a fannin kula da lafiyar al’umma  (Fellowship in Community Medicine) wanda yanzu haka saura kadan in kamala digiri na uku a (West African College of Physician), Karatun da nake gudanarwa a asibitin koyarwa ta Danfodiyo(UDUTH) Sakkwato.”

“A shekarar 2013 na nemi aiki da hukumar lafiya ta duniya watau World Health Organization(WHO)  aiki ya koyamin sanin makamar aikin kiyon lafiya matakin farko mafi karfi a fagen rigakafin cuta da kawar da cutar Foliyo, anan na samu horaswa ta hanyoyin kulawa da lafiyar al’umma bisa tsari wanda duniya ta yarda da  shi.  Mafiyawan aiyukkan da nake yi a  kananan hukumomin jihar Sakkwato ne, a cikin karamar hukuma 23 a halin yanzu 7 ne kawai ban taba aiki ba.” In ji Dakta Larai.

Ta cigaba da cewa “Na samu halartar tarukkan wayar da kai(Conference) a ciki da wajen Nijeriya a Kaduna, Zariya, Kano, Katsina, Lagas, Fatakwat, Kebbi, Zamfara, Abuja, Oyo, Ogun da jihar Taraba. Haka kuma naje kasar Burkina, Thailand, Dubai a kasar Saudiya.”

Ta ce Ta taba jagorantar mahajjatan Sakkwato zuwa kasa mai tsarki a matsayin likitansu har sau uku.

Mamba ce wani lokacin jagora, tana  daya daga cikin jagororin kungiyoyin likitoci da ma’aikatan lafiya kamar NMA Sakkwato Ma’aji har sau biyu,  ARD, MWAN, SMDA, APHPN. A bangaren kungiyoyin cigaban al’umma akwai  kungiyar cigaban matasan Nakasari da kuma wata ta cigaban matan Nakasari da sauransu.

“A hukumar lafiya ina rike da kananan hukumomi biyu zuwa uku, a kowane wata ina aiki tun shidan safe zuwa tara na dare, bayan himma da nake yi wajen taimakawa gwamnatin jiha  da ta kananan hukumomi wajen harkar rigakafin cirutocin kawar da Foliyo da horas da ma’aiktan lafiya da wayar da kan al’umma da kulawa da mata masu juna biyu da kananna yara.”

“Rayuwa ta nuna min yadda ake hulda da jama’a a kowane jinsi tare da la’akari da mutunta kowa gwargwadon hali kuma na fahimci cewa ‘babu maraya sai rago’.”

“Na yi aure da shekara 24 kuma bai hanani karatu ba ina da ‘ya’ya biyar maza biyu mata uku, muna cikin koshin lafiya dukanmu.”

“A matsayina na ‘yar jihar Sakkwato ina jin takaicin  zaman banza da lalaci da maula, haka ma ina bakin ciki duk lokacin da naga  ana zalunci da rashin gaskiya don samun nasarar rayuwa. Ina tsananin kishin jiha ta; ta zamo kan gaba a kowane fanni na rayuwa. Maza matasa da mata su jajirce su zama masu cin gashin kansu ba ci-ma kwance ba, ina mai kwadayin ganin ‘ya’yan Sakkwato sun bayyana a kowane mataki na cigaba a gida da waje don kawar da maula da tumasanci.”

“Ina matukar tausayin talakawa da masu karamin karfi idan sun shiga halin matsi ko kaka nika-yi, in da hali bana ganin hasarar taimakawa da ba da tallafi daidai gwargwadon hali na, ganin yanda nake diyar talakawa na samu tallafi na tsayu da kafafuna, haka nake son sauran jama’a su samu su kafu,  da irin wannna damar su kaucewa kalubalen rayuwa wanda zai iya gurgunta su.” A cewar Dakta Larai baya goya marayu.

Ina godewa Allah tun girmana  ina da jajircewa da naci da yin gaba-gadi ga duk abin da ni fuskanta na rayuwa, ba tare da tsoro  ko jin ce wa ni mace ce in dai manufar ta alheri ce ban damuwa ina shiga, matukar ban samu nasara ba zan sake gwadawa a gaba. Wannan yana da nasaba da addu’ar  iyaye da ‘yan uwa da abokai na gari a kaina, bayan ladabi da biyayya  da tsare gaskiya.

        

Daga Sadiya Attahiru