*Ina matuƙar godiya ga dukkan mutanen da suka kirani don yi mun gaisuwar rashin da mu kai, da masu yi ma Mamana addu'ar samun lafiya, duk na gode sosai da sosai Allah Ya bar zumunci*.
Hauphanku ce
Page 19
"Jiddah kuka ba abin da zai maki, don haka ki share hawayenki ki natsu ki koma ga Allah ki dage da addu'a shi ne mai maganin kowace irin damuwa. Wallahi Jiddah a wannan lokacin babu macen da bata da matsala a gidanta sai dai ta wata tafi ta wata, amma duk wadda zata dube ki tace bata da matsala a gidanta to ƙarya take, yanzu lokaci ne muke wanda babu babba babu yaro kowane gida sai kin samu matsala ko dai ga maigidan ko ga matar gidan. Sai dai kawai mu cika fili da addu'a Jiddah amma don Allah ki daina saka damuwa a ranki ki daina takura ma zuciyarki da tunani saboda kinga kina da hawan jini kuma mai hawan jini ba a son shi cikin damuwa." Tunda Mamar Khairat ta fara min nasiha nayi shiru ina kallonta domin dai Ni damuwata guda, ina na samo aljanu? Ni dai a sanina ban da aljanu sam, kuma wane irin duka ne nayi wa Safiya? Duk da daman naji a lokacin tamkar na kamata na yi mata dukan tsiya lokacin da take gayamin maganganun sai kuma na dake na share ta har kaina ya fara sarawa ban ce mata ƙala ba, don ba zan iya cewa ga abin da ya faru ba Ni a tsakaninmu ba sam.
Sai yamma lis sannan an kawo min tuwon dare daga gidan Maman Khairat, ita kuma ta bi yaran da suka kawo min tuwon suka tafi tana min Allah Ya sawaƙe, har ƙofar gida na raka ta tana ta ƙara min nasiha kan nayi haƙuri watarana sai labari.
Bayan Maman Khairat ta tafi ne nayi alwala na zauna ina jiran kiran sallar magrib naji shigowar mutun ko ban tambaya ba nasan maigidan ne don shi kaɗai ne yake shigowa bai sallama. Haidar ya nufe shi yana kiran Abba amma ko waigen shi bai ba ya shige ɗaki. Ba ƙaramin faɗuwa gabana ya yi ba amma sai na dake na miƙe a hankali na nufi ɗakin, har ya kwanta kan gado yana shafa wayarsa, ga dukkan alama abin da yake yi da wayar nayi ma shi daɗi don sai murmushi yake. Da sallama na shiga ɗakin, da yake akwai wutar NEPA don haka ina ganin yadda nan take murmushin fuskarsa ya kauce ya gayyato ɓacin rai ya shimfiɗa akan fuskarsa. Ban damu ba nasan zan ga fiye da hakan, na isa na zauna gefen gadon nace, "Sannu da zuwa Abban Haidar." Kamar yadda na zata hakan ya faru ko ƙala bai ce ba, na sake maimaita wa sai ma ya saki uban tsaki ya dube ni a fusace yace, "Wai miye daga zuwana za ki isheni da magana?" Kaina na ƙasa nace, "Sannu da zuwa nake maka fa." Ya ɗan tsura min ido sai kuma ya tashi zaune yace, "Da gaske kina da aljanu? Kuma sun bugi Safiya ɗazun?" Girgiza kaina nayi alamar a'a, ɗan tsaki ya sake ja yace, "To wallahi kin ji na gaya maki daga Yau sai Yau kowa ya yi rayuwarsa a gidan nan kar ki sake shiga rayuwata kamar yadda Ni ma ba abin da ya shafe Ni da taki rayuwar." Ban ce ƙala ba ya koma ya kwanta yana tsaki akai-akai.
Haka na dawo falo na gyarama Haidar kwanciyarsa, can cikin barci na ji shi yana kirana, kamar na share sai kuma naga ba kyau, don haka na tashi naje, ba wata magana ya jani jikinsa, ya biya buƙatar sa ya juya ya kama barci. Ba abin da na tsana irin na haɗa jiki da Deeni Allah Ya zuba min tsanar mazinaci na tsani zina don haka na koma falo nayi kukana na gode wa Allah na tashi nayi wankan tsarki na kwanta.
Washegari tunda safe ya bar gidan, ba tare da ya ban ko sisi ba, ga Haidar bai da haƙurin yunwa sai ya tasani gaba ya yi ta kuka, idan yana jin yunwa, hakan yasa na bishi da sauri na ina kiran sunansa, har ya ɗan yi nisa ya juyo fuska murtuk yana kallona baice ƙala ba, cike da ƙwarin gwiwa nace, "Ka manta baka ban kuɗin kalaci ba, kuma naga idan rana tayi ƙarewa yake." Idan bango ya tanka min shi ma ya tanka min, haka ya ƙare min kallo ya juya ya yi tafiyarsa ya barni tsaye ƙofar gidan ina bin bayansa da kallo.
Ko da na dawo gida na ɗauki tsintsiya ina shara kamar wasa naji amai ya taso min, cikin lokaci kaɗan nayi amai sosai har ya kai idan nayi aman sai dai nayi aman yalon ruwa mai ɗaci, ga Haidar na bina yana kukan yunwa, duk na rasa yadda zan yi saboda na fara galabaita sosai da aman. Kafin kace me zazzaɓi ya rufe Ni na lallaɓa na shige falo na kwanta ina jan Haidar jikina shi ma ya kwanta don ban da sanyi ba abin da nake ji, shi kuma kuka yake tamkar ana tsunkulinsa. A haka Maman Khairat tai sallama, ina jinta amma ban da ikon amsa mata sallamar amma har ga Allah naji daɗin zuwanta, ko ba komai zata kama min Haidar na samu na natsu na ji da kaina.
Ai kuwa har da kofin kununta da fanke ta zo, ta zuba ma shi a kofi ta ba shi sannan ya bar kukan ya kama sha yana gwarancinsa na yara.
"Jiddah ba dai tun jiya baki lafiya ba? Ki ka kasa aikawa a gayamin kuma? Ta ya za ki zauna da ciwo ke kaɗai a cikin gida Jiddah?" Ni dai zuwa lokacin ban da kyarma babu abin da nake yi, Saboda baki ɗaya zazzaɓin ya gama rufe Ni jikina ya ɗauki zafi sosai da sosai .
Ina jinta sama-sama ta fice bata jima ba ta dawo, ashe magani ne ta siyo min, ta ɗebo ruwa tace, "Jiddah nasan baki iya shan kunun nan don haka tashi ki sha ruwan shayi ga shi sai ki sha magani kwanciyar ba magani ba abinci ai bata yiyuwa." Ban san magani ko alama don haka nayi kamar ban ji ba, amma ganin ta matsa da magana dole na tashi na amshi maganin nasha da ruwan shayin na koma na kwanta. Sai dai ko gama kwanciya ban ba amai ya ƙwace min ta baka ta hanci, sai da nayi mai yawan da yafi ruwan shayin dana sha sannan ya lafa na koma na kwanta.
Ita ta gyara gun tas, ta fice ta ida sharar dana fara ta tattara kayan wanke-wanke tayi duk ina kwance ina jin jikina na ciwo kamar ana daddaka min shi haka nake ji don haka nake ta juye-juye ga shi ban iya ko ɗaga kaina saboda shi ma ciwo yake sosai. Haka na wuni don haka ta tafi zuwa can ta dawo da mutanen gidansu aka sakamun ƙarin ruwa, suna zaune Deeni ya shigo kamar yadda ya saba ba sallama ya raɓa su ya wuce bai ce ma kowa komai ba, sai su ne suka dinga gaida shi suna tambayar ya mai jikin, ba tare daya kalleni ba yace da sauƙi ya shige ɗaki abinsa.
Ya ɗan jima kana ya fito ya sauya kaya ya fice bai ce ƙala ba. Maman Khairat ta dube ni, "Yaushe maigidan ya dawo ne Jiddah?" Cikin yanayin maganar marar lafiya nace "Jiya ya dawo bayan kin tafi gida." Ta sake kallona "Kuma yasan baki lafiya kafin ya fita?" Kaina na girgiza alamar a'a bai sani ba. "Allah Ya kyauta! Abin da tace kenan tabar maganar.
Wasa-wasa sai da na share kwanaki ina fama da ciwo daga wancan sai wancan a lokacin ne Maman Khairat ta dube ni tace, "Anya kuwa Jiddah ba ciki ne da ke ba? Na lura duk wasu alamomin ciki sun bayyana gare ki fa." Cike da mamaki na waro idanuwa ina kallonta, wane irin ciki kuma? Ni da rabo na da Deeni har na manta inba ranar da ya dawo ba, kuma shi ma a ranar shi kaɗai ya yi kiɗi da rawarsa? Anya kuwa ana samun ciki daga haɗuwa ɗaya? Itama marar daɗi irin wannan haɗuwar... "Ya daga tambayarki kin fara sana'ar taki Jiddah? Yaushe za ki daina tunani ne wai? To ki sani masu ciki ba a san ko da damuwa suna saka kansu a cikin matsala, dama kin ture komai kin natsu kin zauna lafiya."
Cikin sanyin jiki na dubeta nace, "Ba shakka cikin ma zai iya yiyuwa domin Ni dama ba wani ganin jinin al'ada nake ba duk wata ina shafe watanni ban ganshi ba, yanzu haka rabona da shi tun kafin na yaye Haidar Maman Khairat, amma ban da tabbas gaskiya."
"Idan kau haka ne ki tambaye shi gobe sai na raka ki asibiti ai maki awon cikin don mu samu tabbas." Cewar Maman Khairat.
Sai da dare da Abban Haidar ya dawo na iske shi da maganar zuwana asibiti, ban ɓoye mai ba na gaya mai zan je ai min awon ciki ne don ciwon da nake ya yi yawa.
Banza yai da Ni tamkar bai ɗakin, na gaji da jiran ko zai tanka bai tanka ba na tashi na koma falo don tuni mun raba ɗaki yana ƙurya ina falo.
Washegari Maman Khairat ta zo mu je asibiti na gaya mata yadda mu kai tace "Ai ciwo ne mu je kawai." Ai kuwa muna zuwa awon farko aka tabbatar da ina da yaron ciki. Sam ban murna ba, sai naji wani bala'in tausayin kaina, ko yanzu daya nake riƙe da Haidar kawai balle ga wani cikin? Sai nafi sati guda ban kama Naira ɗari ɗin Abban Haidar ba. Ko da yaushe daga gun Mamana sai gun Maman Khairat kawai nake samun ɗauki, sai kuwa Binta wani sa'in takan kawo min abinci har gida ba kamar idan ta ji kukan Haidar ya yi yawa.
Haka muka dawo gida jikina sanyi ƙalau ina tuna haihuwar farko da nayi ta Haidar, yanzu abin ya wuce wancan karon ma tunda yanzu tsakanina da shi sai idan yana da buƙata ta ya kawo min ruwan Lipton da biredin naira ɗari kawai da dare na sha ya biya buƙatar shi da Ni ya kwanta sai kuma ranar da wata buƙatar ta motsa zai sake kawo min ruwan Lipton da biredin. Shi ma da haka kawai yake zuwa sai da na dinga cewa ban iyawa yunwa nake ji idan ya neme Ni yasa yake kawo min Lipton da biredin.
To yanzu ga wani cikin Ni Jiddah ya zan da rayuwata? Haka kullum na kasance cikin ciwo Yau lafiya gobe ciwo. Ga cikin sai ya saka min cin abinci amma ba abincin dole tasa na fara bin gidajen maƙwabtana da sunan zuwa a gaisa amma har a zuciyata abinci nake nema idan sun yi an ban in amsa. Ban dai iya zuwa roƙon abinci kai tsaye don ina jin matuƙar kunya da nauyi.
BAYAN WATA TARA***
Cikina ya isa haihuwa, amma ban da kayan jarirai na gwanjo da na samu na siya gun wata maƙwabciya ba abin da na tanada, haka gidanma ba komai na ci irin fannin abinci komai babu, haka nake ta rarrakawa har dai cikin ya kai wata tara ban aje ba haka ban ba wani ajiya ba, maigidan kuwa tunda na ba shi takarda ta gwajin cikin da akai min bai min magana ba, ko yace ashe ciki gareki ko ya yi min sannu idan ina amai ko zazzaɓi bai taɓa ba, don haka nima na kawo idanu na saka mai kawai muke tafiya a hakan. Ba wata magana ko hira balle wasa da dariya tsakanina da shi sai idan buƙatar shi ta motsa kawai zai neme Ni.
Ba don nasan cewa ba idan na hana shi kaina ba ina da tarin zunubi ba da ba abin da zai sa na yarda da shi, saboda dama kwata-kwata ban san daɗin abin ba, kawai ina biye mai ne don na hana shi yawace-yawace, saboda yadda na tsani zina a raina yasa duk rintsi ban hana shi kaina. To tun da na gane yana kula wasu matan sai abin ya ida kubce min baki ɗaya na tsani harkar ban sha'awa ban jin daɗi haka sai nayi kuka duk bayan ya kusance Ni, sau tari ma yana cikin yi ina kuka saboda baki ɗaya tsanarsa da tsanar harkar ke yawo a jinin jikina.
Ranar Talata ina zaune naji cikina ya fara murɗawa kafin kace me? Marata itama ta amsa na rasa inda zan sa kaina. Ba zan iya misalta irin ciwon da nake ji ba, ina cikin halin Binta tai sallama da gudu ta koma ba a jima ba sai gata da Mamar Khairat sun shigo.
Ganin halin da nake ciki yasa Maman Khairat kiran mijinta da yake yana da mota, kai tsaye asibitin kuɗi ya nufa da Ni. Awon farko suka ce haihuwa ce amma jinina ya hau sosai ba zan haihu yanzu ba. Mijin Maman Khairat ya je ya nemi Abban Haidar ya gaya mai ban lafiya ina asibiti ya gaya mai sunan asibitin haka aka aika gun Mama aka gaya mata, har Yayarta ta zo amma ba Deeni ba labarinsa sam bai zo ba haka daga gidansu ba wanda ya zo.
Har na kwana biyu asibitin ba Deeni ba ƴan gidansu, sai ana ukku na haihu yara biyu duk mata. Cikin ikon Allah sai hawan jinin ya sauka aka sallame mu.
Mijin Maman Khairat ya dube ni yace "Gidanki zan kai ki ko gidan iyayenki?"
Hawaye suka zubo min. Tabbas da ace ina da gata gidan iyayena ya kamata na nufa tunda aka kaini asibiti kwana biyu banga idon Deeni ba haka ba wani daga gidansu da ya zo dubani amma bayan can ina ne zan nufa? Sai nace a kaini gidansu Babana tunda can ne dole ne Mamana itama yanzu Babanta ya aura mata abokinsa ba jin daɗin zaman gidan aurenta take ba, duk da bata gayamin amma ina lura da yadda duk ta lalace ta rame ta fita hayyacinta baki ɗaya tamkar ba ita ba. Idan na je ma haƙuri zata ban kawai tace na koma ɗakina don haka gwara gidan Babanmu idan suka koran sai na koma gidana... "Fito mun zo." Cewar Maman Khairat kenan bayan mun je ƙofar gidansu Babana.
Yana zaune matasa kewaye da shi, suna ta labari, rabona da shi tun ranar da Hajjo ta kawo Ni daga Kano sai Yau.
Har ƙasa na duƙa na gaida shi, ya amsa ya dubi yaran dake zaune gunsa yace, "Wacece wannan ɗin da take gaidani?" Cikin tsananin tashin hankali na ɗago na kalli mahaifina ido cikin ido wai nice bai gane ba, nice yake tambayar wacece? Ɗaya daga cikin yaran yace, "Jiddah ce fa ƴarka Oga baka gane ta bane?" Cikin ko'in kula yace, "Ai wai Jiddah ce daman? Daga ina haka to? Dama an gaya min kin yi kuɗi ba a san inda kika samo su ba ma kin kama sana'a ko?" Kasa magana nayi domin ban zaci hakan daga mahaifina ba duk da nasan cewar bai sona amma ban san rashin son har ya kai hakan ba ai. Don haka bance komai ba na miƙe da ƙyar ina share hawayena na nufi cikin gidan nabar Mamar Khairat na miƙa ma shi yaran na gaya mai haihuwa nayi. Ban san ya suka ƙare ba na shige jikina sanyi ƙalau. Kakata na zaune na shiga tana cin zogale amsa sallamar tai kanta na duƙe ta ɗago muka haɗa ido, nan da nan ta haɗe rai ta cigaba da abin da take, hakan yasa na gaidata ina shirin tafiya Mayman Khairat ta shigo rumgume da yarinya guda Babana ɗauke da guda.
Yana washe baki ya miƙawa Innarsa jaririyar, "Ashe Jiddah haihuwa tai yanzu daga asibiti suke Inna yara biyu ta haifa duk mata." A kan fuskarsa na fahimci ya ji daɗin haihuwar don sai fara'a yake, sai a lokacin na ɗan ji dama-dama a raina. Maman Khairat ta gaida Kakar ta cigaba da kora masu jawabin na kwana biyu asibiti ban lafiya an gayama Deeni amma bai je ba haka wani na shi bai je ba, don haka dana haihu nace a kawo Ni nan gidan... "La ila ha illallahu! To idan an kawo ta nan gidan wani abu za ai mata ko ai ma shi ne?" Cewar Kaka data katse Maman Khairat daga maganar da take. Cike da gadara Kakar tace, "Mun ga yara Allah Ya raya amma maza ku tashi ki nufi gidanki ɗakinki idan kin ƙi kuwa ki lalace a banza. Yo wai zaman me za ki zo ma ki yi a cikin gidan nan nace?" Ganin tana ta masifa yasa na miƙe hawaye na zuba na kalli Maman Khairat nace mu je kawai. Haka ta biyo ni baya muka fita na shiga motar na ida sakin kuka mai cin rai. Tun yanzu kenan ina ga can gaba? Me yasa wai ban da sa'ar rayuwa ne Ni? Me yasa komai nawa ya fita daban da saura? Har muja je gidana ba wanda ya yi wa wani magana sai mijinta kawai da yace, "Allah Ya sawaƙe!
Bamu jima da zuwa gidan ba mutane su kai ta zuwa ganin jarirai. Maman Khairat ta ban kuɗi Naira dubu goma tace In ji Babana. Naji daɗin kuɗin tunda ban da su haka akwai buƙatar su don haka nace ta riƙe gunta tai duk abin da ya kamata da su.
Ta fice kenan sai ga Abban Haidar ya shigo nasan tunda ya ga mutane ranshi ya ba shi an haihu ne.
Ina zaune kan gado ya shigo ina kallonshi ya tsaya yana ƙarewa yaran kallo, amma tsabar girman kai yasa ya kasa furta ko da kalma guda ce gare Ni.
"Sannu da zuwa Abban Haidar." Ina dubansa amma sai ya yi shiru kawai, ƙarshe ma sai ya wuce ya ɗauki yarinya ɗaya yana kallo sai kuma ya aje ya ɗauki ɗayar, ina kallonsa ya fito da waya yana ta ɗaukar su hoto yana murmushi. Ya gama ya sake kaya ya fice ina jinsa yana waya yana cewa matarsa ta haihu an samu yara biyu duk mata.
Bai jima da fita ba aka ce min motar icce ta zo, yara su ka dinga shigo da icce nasa ma shi ne ya siyo har naji dama-dama a raina,sai ga Maman Khairat da kaya niƙi-niƙi yara na biye da ita. Bayan nai mata sannu ta jani inda ba mutane tace, "Jiddah kuɗin da Babanki ya bada ne na siyo icce na siyo maki kayan abinci wanda za ki ci kafin bakwai sai madarar jarirai don nono kawai ba isar su zai ba nasan."
Sai jikina ya yi sanyi kuma, kenan ba daga gun Deeni iccen yake ba ? Tabdijam kenan wannan ma haihuwar kamar waccan zata kasance? Na girgiza kaina ina jin cewar insha Allah na gama haihuwa a gidan Deeni har abada zan ƙare rayuwata da yarana uku.
Sai yamma lis ƴan gidansu Deeni suka zo min barka, ban damu ba, domin ba tasu nake ba, dangin mahaifiyata da mutanen unguwa da wanda nake abin arziƙi da su tuni sun cika min gida ana ta harkar arziƙi. Yayarshi ta ware Ni gefe guda take tambayar wai dame-dame Deeni ya kawo gidan? Nai murmushi nace ban san me zai kawo ba tukun tunda Yau akai haihuwar.
Ta fiddo ido waje, "Kai amma Deeni bai ji daɗin halinsa ba, tunin duniya fa yace ya gama haɗa komai ke kawai yake jira ki haihu." Cike da takaici a ƙasan zuciyata nace, "Ba mamaki suna can gidan naku ya aje amma nan bai aje min komai ba." Gabana taita maganganu marassa daɗi kan Deeni Ni dai ban tanka ba, saboda zuciyata ta riga ta dake yanzu ban jiran komai daga kowa na fawwala Allah lamurrana duka nasan shi ne kawai zai min maganin duk wata damuwata .
Cikin dare Mamarsa ta zo taita faɗa tana ban haƙuri, tace zai je ya sameta, Ni dai haƙuri kawai nake bata don ban da ta cewa (Ɓarawo hannun mata) ta gama faɗanta sosai tace zata aiko min da geron damun kunu da masara a dinga tuwo da dare nai mata godiya ta tafi.
Sai ga gero da masara kuwa yara sun kawo na amsa na aje ina ƙara gode wa Allah daya rufa min asiri ban kasa samun abin da zan ci ba a wannan haihuwar ba.
Cikin dare ya dawo har nayi barci ya tada Ni cike da bala'i yake cewa, "Ke har kin isa ki haɗa Ni da mahaifiyata ne? To akwai uban daya isa yasa Ni yin abin da ban yi niyya bane ba? Ban da rainin hankali irin naki ma Ni nasan ma lokacin da za ki haihun ne? Ba kawai don an ɗauke Ni ɗan iska ba sai aka same Ni aka gayamin wai kina asibiti baki lafiya don kuma an ɗauke Ni ɗan iska sai aka kai ki asibitin kuɗi tunda ga Sakarai ko? Ai shi yasa na ƙyale ku naƙi zuwa." Ni yanzu faɗan Deeni bai damuna don haka har ya yi abin sa ya gama ban tanka mai ba, sai da ya dube ni yace "Yara kuma ɗaya ta ci sunan budurwata Safiya ɗayar kuma sunan ƙawar Safiya ne A'isha." Idona waje nace "Gaskiyar magana ban san suna ko guda a cikin sunayen sai dai a sake wasu amma baka saka min sunan Safiya da ƙawarta a yarana haka kawai su kwaso mugayen halayen masu sunan." Har ya wani zaburo zai kawo min duka sai kuma naga ya janye hannunsa ya buga tsaki yace, "Tunda yaran naki ne ai sai ki sauya masu sunan. Ke bari ma ki ji ba dan Safiyar taban haƙuri ba wallahi da ban yi masu yankan sai da tasa baki sannan na amince zan masu yanka amma da yake baki da godiya baki san mutunci ba shi ne don ta zaɓi sunayen da za a saka ma yaran za ki ce baki so, to wallahi sai an sa su ki mace idan an gaya maki sunayen ranar sunan."
Daga haka ya gyara kwanciyarsa ina jinsa ya kira waya wadda nasan mace ce ya kira daga jin yadda yake tambayar ta batai barci ba?.
Wannan karon ma Hajjo daren suna ta zo sai dai ba ta kawo min kayan abinci kamar wancan karon ba ta dai zo da sutura na yaran da nawa masu kyau ko Ni kala shida ta kawo min yaran kuwa akwati biyu aka kawo masu hatta Haidar an kawo ma shi kala biyar masu kyan gaske.
Washegari ranar suna ina ta jiran naji sunan yara sai ga shi kam ance min an samu Safiya da A'isha. Hawaye suka zubomin Mamar Khairat ta tambayeni abin da ya faru na gaya mata yadda mu kai da Deeni kan sunayen yaran. Ta girgiza kanta tace, "Manta da shi duk sunan da Uwa take kiran yaranta da shi to ba shakka shi ne ke bin yaran don haka ki zaɓi sunayen zamani masu daɗi ki dinga kiran yaranki da su, sai an wayi gari idan ba makaranta ba babu wanda zai san asalin sunayen yaran."
Hajjo dake zaune ta gyara zama tace, "Kai anyi ɗan ƙwal uba yaron nan Deeni, amma ai idan yasan wata bai san wata ba, shin akwai masu yin sticker ta haihuwa nan garin? Idan akwai a kira min shi ya zo ya yi wa yaran sticker ya sa masu suyanen da ake so sai inga ta iskanci."
Nan da nan kuwa Maman Khairat ta kira mai masu hoto ta tambaye shi yace ai yana yi anyi sa'a kuma yanzu zai je fitar da wata don haka bari ya zo ya haɗa sai ya kawo ta yanzu insha Allah.
Mai hoto ya zo ya yi wa yara har ma muma akai mana ya tambayi sunayen yaran da za a saka na gaya mai Safiya ya saka mata nickname ɗin (Afnan) A'isha kuma yasa mata nickname ɗin (Afnah) kowa yace kin yi daidai kuwa Jiddah sunaye masu daɗi irin na ƴan boko kuwa.
Wajen sha biyu aka shigo da Tumaki guda biyu na yanka ba laifi suna da ɗan girma, Hajjo ta dube ni tace, "Shin anyi wa Haidar yanka kuwa daga baya Jiddah?" Kaina na girgiza nace, "Ba ai ma shi ba Hajjo." Ta muskuta ta fiddo kuɗi masu dama ta ba Maman Khairat tace "Ƙirga min nan ki ga ko nawa ne ki ba mijinki a nemo min rago a haɗa ai ma Haidar yanka bako ɗaya." Dubu ashirin da biyar ne cif cewar Maman Khairat. Ta miƙe kuwa ta fice zuwa aiken Hajjo.
Ba a wani jima ba sai ga uban rago mai girman gaske an kawo, ba kunya sai Deeni ya kira Ni wai zai kama tunkiya guda ya saida tunda ga wani rago ya gani. Na kada baki nace ai Ragon na Hajjo ne zata yanka ma Haidar tunda ba ai mai yanka ba.
Ya ɗan tsura min ido, "Da gaske Hajjo ce ta bada kuɗin Ragon?" Cike da ƙwarin gwiwa na tabbatar ma shi da haka ne.
Ya ja tsaki, "Waccan tsohuwar na shigar min hanci Wallahi." Sanin zai iya faɗin abin da zai sosa min rai yasa na bar gun na koma gun mutane aka ci gaba da harkar arziƙi.
Ana ta taron suna Deeni ya aiko na bada ƴan ciki da abincin suna akai ma shi. Na gayama Maman Khairat a zuba mai, ta dube ni tace "Ya bada wani abu ne bayan Tumaki? Nace a'a bai ba da ba, amma idan ba a kai mai ba yana iya zuwa cikin mutane ya yi min tujara.
Tace "Allah Ya sawaƙe! Ta samu manyan kuloli ta zuba komai ta ba yara su kai sai Hajjo ta hango ta kuwa ta so tace, "Ina za a kai wannan abincin?" Maman Khairat ta gaya mata yadda mu kai. Hajjo ta ja tsaki tace ma yaran "Maza ku kai abincin gidan mahaifiyarta kuce "Ga shi nan in ji ni taba nata mutanen." Ga kawo Naira ɗari taba yaran ladan aike.
Suka kuwa tafi suna murna.
Hajjo ta ɗauki farar leda ta tsinci ƴan hanjin rabin laida ta ƙulle ta ba wata yarinya tace maza ta kaiwa Deeni tace ya bada kuɗin magi da man da aka sakama naman, abinci kuwa muna jira ya kawo a dafa mai."
Hatta hantar cikina sai da ta kaɗa don jin abin da Hajjo tai ma Abban Haidar, amma ya zan dole na shige ɗaki gun mutane ina jiran amsar da Deeni zai maido.
Mai hoto kam ya cika alƙawari sai ga shi ya kawo nan take akai ta ba mutane, kowa nata yaba sunayen wai na ƴan gayu ne.
Shiru-shiru Deeni bai sake aikowa ba, tun ina tsammani har na daina, abin ya ban mamaki sosai, domin na ɗauka sai ya zo da kanshi yayi ruwan rashin mutunci amma shiru.
Bayan taron suna ya watse aka fito da duk abin da na samu tas. Hajjo ta dube ni tace, "Iyayenki sun bada dubu hamsin na kawo maki sunan a wajena, sannan Uncle Salim ɗinki ya bada kayan abinci yace a kawo maki, amma ban kawo maki su nan ba, domin an gaya min yadda mijinki ya sace waɗancan kayan abincin ya saida ya amshe kuɗaɗen ya kashe ya barki kina ta gararanba ba abinci ba sana'a. To wannan karon yadda na zo da kuɗin nan da su zan koma Kano, amma bayan kin gama wanka yaranki sun yi ƙwari ki shirya ki je Kano zan kai ki kasuwa ki yi sarin kaya ki dawo ki ci-gaba da sana'arki Jiddah kin ga dai wannan karon yara biyu Allah Ya azurtaki da samu, zama ba sana'a ba naki bane ba, bin makwabta neman abinci ba naki bane ba, Jiddah ki zama jaruma, ki zama tsayayyar mace wadda zata ji da duk matsalolinta wadda zata tsaya kan ƙafarta akan duk wasu buƙatunta, kinga dai yadda Allah Ya juya lamarin Mahaifiyarki ya kaita inda ba daɗi inda take fama da kanta to bai kamata ba ace Uwa kwance ƴa kwance ba, ya kamata ace kin zama jajirtatta wadda za ki share hawayenki ki share na Mahaifiyarki Jiddah."
Nayi na'am da shawarar Hajjo kamar yadda kowa gun ya yi na'am da ita, nayi godiya sosai nace ai ma iyayena godiya suma. Hajjo ta sake fiddo waya mai kyau tace In ji Uncle Salim na kaima Mahaifiyarki tata ita ma tare ya sai maku yace akwai lambarsa a ciki ko da kina buƙatar kiransa."
Allah Sarki Uncle Salim! Yana matuƙar tausayina yana min abin da mahaifina bai min, don haka kallon mahaifi nake ma shi ko da yaushe.
Yau sam Deeni bai dawo ba kamar yadda ya yi a haihuwar Haidar har Hajjo ta kore shi Yau bai zo ba. Hajjo tace ya kyautawa kansa don idan muka haɗu sai ya biyani kuɗin da ya amsa munafikin ."
Washegari akai suyar nama aka gama aka fitar dana gidansu Deeni dana gidansu Babana har da na Babana kanshi sannan aka fitar dana Deeni suma kowa ya ɗauki nashi aka fitarma da Mamana da nata.
Ba laifi an aje min nama mai yawan gaske, suka ɗaga gadona suka saka aka aje marar yawa a fili saboda Deeni.
Sai da suka gyaramun komai na gida suka tafi Hajjo ta ban dubu goma tace na riƙe a hannuna ko da zan nemi wani abu, kayan abincina kuwa za a dinga aiko min daga gun Mamana duk bayan lokaci.
Ɗaki na shige na tasa yarana gaba ina kallo Haidar na zaune nata wasa, Abban Haidar ya faɗo gidan. Kallo guda nai mai na kauda kaina na bishi da sannu can cikin maƙoshina don har ga Allah ban san kallon fuskar Deeni yanzu wata muguwar tsanarsa ke bijiromin duk lokacin dana sauke idona kan shi.
"Ke wai me kike nufi ne da aka hanani abincin suna jiya kuma baki ce komai ba? Me ya hana ki sa akai ma Safiya ita ma? Wallahi Jiddah idan kika sake sai na baki mamaki a cikin gidan nan."
Idan bangon ɗakin ya tanka nima na tanka, na yi kamar ban ji shi ba.
Ganin hakan yasa ya fara bincike cikin ɗakin, namanshi ya gani ya ɗauka, ya fara jujjuya shi "Wai kina nufin dabba uku ɗan abin da za a ban kenan? Ya banga buhunnan kayan abincin ba? Ina kayan da kika samu ke? Ai naji gidanmu ana cewa kin samu kuɗi da kaya duk suna ina?"
Cike da takaici na dube shi nace, "Abincin suna ka kawo ne da zan zuba na kai ma? Naman suna kuma ina ruwanka da Ragon ai naga tumaki ne kawai naka ko? Kayan da na samu kuma Ni na samu ba kai ba, don haka gudun munafikin ɓarawon daya sace min na wancan karon yasa wannan karon adana kayana don ya je ya saci na Uwarsa idan ya tashi satar. Kuɗi kuma ba damuwarka bane jin yadda nayi da su ba tunda babu sisin kwabo da suke da sunan naka ne duk biki ko sunan da nake zuwa baka taɓa ban naira ba kace na kai ba balle yanzu don an maido min biki kace na baka. Safiya kuma ban kai mata ba, idan Uwata ce Yau ba sai gobe ba ta tsine min albarka nabi duniya saboda na hanata kayan sunan yarana."
Baki da hanci ya buɗe yana kallona har wani firgici na karanta a ƙwayar idanunsa wanda nasan ba na komai ba ne sai na maganganun dana sakar ma shi ne.
To fa masu karatu Jiddah ta ɗebo da zafi fa.
Daga taku a kullum Haupha!!!