An saki ‘yan Najeriya 3 bayan shafe watanni 10 a gidan yarin Saudiyya bisa laifin safarar miyagun kwayoyi
An sallami wasu mata uku ‘yan Najeriya da aka kama tare da gurfanar da su gaban kuliya bisa zargin aikata laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya, bayan shafe watanni 10 a tsare, an wanke su daga laifin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya bayyana muhimmancin huldar diflomasiyya da ta kai ga sakin matan.
Matan—Hadiza Abba, Fatima Umate Malah, da Fatima Kannai Gamboi—an kama su ne a ranar 5 ga Maris, 2024, a filin jirgin saman Prince Mohammad bin Abdulaziz, Madina.
Tsare nasu ya biyo bayan kama wasu ‘yan Najeriya biyu da aka same su dauke da kwayar hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.69.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya