A yau kusan wata biyar da yaye jami'an tsaron jihar Sakkwato amma har yanzu ba a ga tasirin kafa rundunar ba, saboda an ƙi ba su kayan aiki da za su taimaka ga aiwatar da abin da ya sa aka Samar da su a cikin jama'ar su.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta yi nata kokakri wurin ganin ta samar da kwararrari da za su kula da shirin amma har zuwa yanzu tsammanin da ake da shi na rundunar ta fara aiki abin ya ci tura.
Yunƙurin da gwamnatin jiha ke yi na ganin an dawo da tsaro a ƙananan hukumomi 13 na jihar da ke fama da matsalar tsaro da ya yi sanadin rasa rayukkan ɗaruruwan jama'a da kuma jefa dubban mutane zama 'yan gudun hijira, yayinda mata da yara sun zama zawarawa da marayu.
Rundunar Tsaron Sakkwato ta samu horo da yanda za ta riƙe kayan aiki domin taimakawa jami'an tsaro ƙasa don tabbatar da samun zaman lafiya da biyar doka da oda a cikin al'ummar su ta hanyar samun bayanan sirri.
In ba a manta ba gwamnatin jiha ta samar da motocin aiki guda 30 da babura 700 ga rundunar bayan ofisoshin ma'aikatan a dukkan jiha.
Sai dai ƙwararren da aka ɗaurawa nauyin ne ya kasa cika alkawarin da aka yi da shi, waton samar da kayan aikin da jami'an za su kare kansu ga farmakin ɓata-gari.
Akwai zargin da ake yi ƙwararren yana son samar da kayan ne ta ɓarauniyar hanya abin da jami'an gwamnati ba su aminta da hakan ba, sun yi tsayin daka a samar da kayan aiki saman hanyar da ta dace.
Masu kishin jihar Sakkwato sun nuna amincewarsu ga samar da kayan aiki bisa ga doka da ƙa'ida, saboda rundunar an samar da ita ne ga doka don haka duk abin da za a yi wanda ya shafe su ya zama kan doka ne.
Ba zai yiwu su riƙa gudanar da aikinsu tare da makamai da ba su da amincewar hukuma ba, kai ka ce wasu ne da ba su san doka ba.
Akwai bayanin da yake yawo cewa ƙwararren da aka baiwa aikin ya shirya da wani ɗan kasuwa ya kawo masa kayan, rashin cika kuɗin mai sayar da kayan ne ƙashin bayan tsaikon da aka samu.
Muna kira gwamnatin jiha ta ɗauki matakin da ya dace kan wannan kwangilar in har ɗan kwangilar yana da dalili mai kyau kan tsaikon da aka samu, duk da haka akwai buƙatar duba lamarin domin abu ne na gaggawa rashin tura jami'an yana sanya su rasa karsashin aiki hakan kuma zai haifar da ƙwarewar su ta tafi a banza.
Rubutu ne na 'yan asalin jihar Sakkwato da suke kula halin da take ciki.