Za mu ci zaɓe a 2023 duk da matsalolin tsaro a Nijeriya -- Abdullahi Adamu

Za mu ci zaɓe a 2023 duk da matsalolin tsaro a Nijeriya -- Abdullahi Adamu

Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023 duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa.

Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan matsalolin, musamman na tsaro, ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen a duniya.

Ya bayyana cewa "Ba shakka akwai taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa taɓarɓarewar darajar naira ba wai mu muka haddasa ta a nan ba, batun tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya."

Sai dai ya ce duk da haka gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin an magance matsalolin.

Najeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro a sassan ƙasar.

A cewarsa, Jam'iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam'iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu.

Taƙaddamar kan ƴan takara Musulmai
Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sai dai ya ce suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra'ayin ƴan ƙasar ga amincewa da wannan zaɓi.

Ya ce zai yi wuya a iya shawo kan al'ummar ƙasar kan wannan haɗi saboda "an samu wani hali ne a ƙasar da ko me ka ce, akwai waɗanda suka lashi takobin ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su" amma tun da ana kan tsarin dimokraɗiyya ne, kowa yana da ikon ya riƙe ra'ayinsa.

Taƙaddama tsakanin CAN da limaman Kirista kan halartar taron APC
Ya bayyana cewa Ubangiji ne kaɗai ya san abin da ya sa mutane da dama suka yarda a zuciyarsu cewa haɗin Musulmi da Musulmi shi ne alheri a halin da ƙasar ke ciki.

Shugaban na jam'iyyar APC ya ce abu ne mai wahala ka iya samun goyon bayan jama'a ɗari bisa ɗari kan wani ƙudiri a don haka abin da za su fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za su gamsar da ƴan ƙasar kan tsarin takarar Musulmi da Musulmi.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce ko kaɗan Jam'iyyarsu ta APC ba za ta sake ta yi asarar takarar sanata a mazaɓar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta arewa-maso-yamma ba, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ce APC ba ta da ƴan takara.

Ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda yana gaban kotu.

A makon jiya ne INEC ta bayyana cewa APC ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

A cewar INEC, APC ta dora sunayen Sanata Ahmad Lawan da Godswill Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC sai dai hukumar zaben ta yanke cewa mutanen biyu ba su aka tsayar ba a zaben fitar da gwanin jam'iyyar.