Zan Tsaya Takarar Gwamnan Sakkwato A 2023-----Sanata Gobir

Zan Tsaya Takarar Gwamnan Sakkwato A 2023-----Sanata Gobir
Sanata Gobir

 

Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir dake wakiltar Sakkwato ta gabas a majalisar dattijai dan jam'iyar APC ne ya yi magana kan matsayarsa a zaben 2023 dake tafe domin cigaba da wakiltar al'ummar jihar Sakkwato.

Sanata Gobir a zantawarsa da Managarciya a gidansa a jihar Sakkwato ya ce "matukar mutanen jihar Sakkwato suka nemi da in tsaya takarar gwamna, zan karba kiransu, da yawan mutane suna kira da na fito takarar ina nazari ne sosai a kai, ina fariciki da mutanen da ke matsamin na fito takarar don hakan ba wani abin kyama ba ne, kan haka zan yi," a cewar Sanata Gobir.

Da yake karba tambayar da aka yi masa kan ra'ayinsa game da kin sanya hannu da shugaban kasa ya yi a zaben kato bayan kato ya ce "bari na sanar da kai mafiyawan Sanatoci a majalisa sun tafi kan a yi gaban kai a tabbatar da dokar waton a sha gaban shugaba Buhari, sai dai ba mu san abin da gobe za ta yi ba rinjaye ka tabbata, mun tafi kan zaben kato bayan kato saboda shigar da kowane dan kasa a cikin tsarin fitar da 'yan takara, zaben daligate ya takaita ne kan wasu mutane kadan yana da kyau ka shigo da kowa shi ne dimukuradiyya, wanda ya samu nasara ya sani wanda ya fadi haka ba maganar zuwa kotu," a cewar Gobir.

Ya yi magana kan 'yan bindigar da suka addabi yankinsu yakamata gwamnati ta yi masu ruwan wuta na kare dangi, a kuma ayyana wasu daga cikinsu matsayin wadan da ake nema ruwa jallo hakan zai samar da zaman lafiya a yankin, 'wannan ne muke bukata a yanzu gwamnatin tarayya ta ayyana mafiyawansu matsayin wadan da ake nema, in aka yi haka da yawa magoya bayansu za su gudu anan an samu hanyar kama su sai kowa a yi masa hukunci daidai laifin  da ya aikata," Sanata Gobir.