Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, dake wakiltar mazabar Gombe ta arewa a Majalisar Dattawa ya bayar da kyautar Motoci da Babura da injunan ban ruwa ga al’ummar yankin mazaɓarsa.
Sanata Alkali, ya raba Motoci 50 ne da Babura 500 da injimin ban-ruwa na noman rani guda dari 600 da kekunan ɗinki da Firji 600 ga mata dake yankin mazaɓarsa.
Sanata Alkali, ya ce cikin ayyukan da ya gudanar a yankin sa baya ga raba wannan talalfi sun hada a wani roko na musamman daga hukumomin asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya FTH da FCE (T) Gombe na ya kai musu dauki wajen samar musu da hanyoyi inda ya yi kokari ya tura rokon nasu a kasafin kudin shekarar 2020/2021 na hukumar FERMA inda ya samu shiga kuma tuni aka yi wadannan hanyoyi.
Ya kuma bayyana ayyuka da dama da ya gudanar a kananan hukumomi biyar da suke karkashin mazabar sa da suka hada da Dukku, Funakaye, Gombe, Kwami da kuma Nafada, inda ya samar musu da cibiyoyin kula da lafiya da azuzuwan karatu da rijiyoyin burtsatse na zamani da masu aiki da hasken rana da tiransifomomi na wuta a wasu yankunan karkara.
Daga nan sai ya godewa shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan na yadda ya samu lokaci ya halarci wannan taro da wasu Sanatoci da suka mara masa baya dan taya shi murnar gudanar da wannan biki.
Wannan yunƙurin na Sanatan abin yabawa ne ganin hakan zai tainaki 'yan saiyasa ga samun romon dimukuraɗiyya.