Kamfanin jirgin sama na Emirate zai dakatar da jigila a Nijeriya

 Kamfanin jirgin sama na Emirate zai dakatar da jigila a Nijeriya

 

Kamfanin jirgin sama na Emirates ya sanar da cewa zai dakatar da jigila a Nijeriya daga ranar 1 ga watan Satumbar 2022.

BBC Hausa ta rawaito cewa Emirates ya dauki matakin ne saboda gaza fitar da kuɗaɗensa da su ka maƙale a Nijeriya.

Idan za a iya tunawa, kamfanin jirgin saman ya aike da wata wasika zuwa ga Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, cewa zai rage zirga-zirgarsa daga sau 11 zuwa 7 daga tsakiyar Augusta saboda makalewar da kudadensa da suka kai dala miliyan 85 a Najeriya suka yi.

A bisa yarjejeniyar da aka cimma da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, ana so su rinka sayar da tikitinsu da naira maimakon kudaden kasashen waje.

Cikin sanarwar da kamfanin jirgin na Emirates ya fitar ranar Alhamis, ya ce zai sake nazari a kan matakin idan har an samu wani ci gaba.