Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Messi da ya lashe kyautar Ballon d'Or sau bakwai ya gamu da koma baya sakamakon rashin sanya sunansa a cikin jerin zaratan yan wasa 30, da ke takarar lashe kyautar da ake bai wa dan wasa mafi nuna hazaka a shekara..
Messi da ya koma PSG ta taka leda tun shekara ta 2006, yake shiga cikin jerin yan wasan da ke takarar lashe kyautar yayin da a bara aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe kyautar,
Kazalika tun shekara ta 2007, yake shiga cikin jerin yan ukun farko da ke takarar lashe kyautar in ban da shekara ta 2018,
Sai dai a bana Messi mai shekaru 35, bai samu shiga cikin yan takarar ba, bayan ya da ya sauya sheka daga Barcelona zuwa PSG ta Faransa,
Tun dai da ya koma PSG daga Barcelona dan wasan ya gaza nuna wata bajintar a zo-agani a kungiyar ta Faransa wadda ke kishirwar lashe kofin gasar zakarun Turai hasali ma kwallaye 11 ya iya zurawa a raga a PSG din,
A ranar 17 ga wannan wata na Agusta ne za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan na bana a birnin Paris na Faransa,
Karim Benzema dai shi ne kan gaba a jerin yan wasan da hasashe ke nuna cewa za su iya lashe kyautar ta Ballon d'Or a bana ganin yadda ya taimaka wa Real Madrid wajen lashe gasar zakarun Turai da ta gabata,
Kazalika akwai Cristiano Ronaldo na Manchester United da shi ma ke cikin masu takarar a bana,
Sai kuma Thibaut Courtois da Casememro da Luka Modric da Vinicius da kuma Antonio Rudiger,
Kazalika akwai Trent Alexander-Arnold da Luis Diaz da Fabinho da Sadio Mane da Darwin Nunez da Mohammed Salah da Kuma Virgil Van Dijk,
A bangaren mata yan wasan tawagar Ingila da suka lashe gasar cin kofin kasashen Turai ta mata a bana da suka hada da Millie Bright da Beth Mead da Lucy Bronze na cikin wadanda aka zabo domin fafatawa wajen lashe kyautar ta Ballon d'Or bangaren mata kenan,