Majalisar Waƙillai na bincikar Ma'aikatar Noma kan Naira biliyan 18 da aka kashe wajen sharar jeji
Kwamitin majalisar wakilai kan asusun jama'a yana binciken ma'aikatar noma kan bada kwangilar da aka ce ya kai kimanin Naira biliyan 18.9 ga kamfanoni yayin kulle-kullen COVID-19.
A zaman binciken da aka yi a ranar Talata, shugaban kwamitin, Oluwole Oke, ya ce an bayar da kwangilar ne ga kamfanoni domin aikin sharar jeji, fitar da filaye da kuma gyara dakunan gwaje-gwajen ƙasa da shuka.
Kwamitin na binciken ne bayan tambayoyi daga ofishin babban mai binciken kuɗi na tarayya kan ma’aikatu da hukumomi (MDAs).
“A yayin kullen da aka yi a kasar sakamakon COVID-19, wasu kamfanoni sun karbi kwangilar kimanin Naira biliyan 18 don share daji daga ma’aikatar noma ta tarayya don fitar da filaye, gyara dakin binciken shukar kasa da sauran su. Amma ba za mu ari bakinsu mu ci musu albasa ba,” in ji Oke.
“Don haka, mun gayyace su da su zo su mu ji nasu bangaren ta hanyar mayar da martani kan batutuwan da kuma nuna mana wuraren da ya kamata su share. Dole ne su kai mu mu ga ƙasar da suka share.
“Mun gayyaci ma’aikatar noma kuma sun gabatar da jawabi. Sai dai wasu daga cikin mambobinmu da ya kamata a ce an yi wadannan ayyuka a mazabunsu sun nuna shakku kan wanzuwar wadannan ayyuka, kuma don jin ta bakinsu, mun gayyaci kamfanonin da suka samu kwangilar da su zo su shaida wa wannan kwamiti inda da kuma lokacin da aka gudanar da ayyukan."
The Cable
managarciya