Majalisar Dokokin Edo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar 

Majalisar Dokokin Edo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar 

Majalisar Dokokin jihar  Edo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, a yau Laraba.

Shugabar masu rinjaye a majalisar,  Charity Aiguobarueghian (PDP Ovia North-East 1), wacce ya bayyana sanarwar tsige Mista Shaibu a ranar 5 ga Maris, ta samu sa hannun mambobin majalisar 21 daga cikin 24.

Ya kara da cewa karar ta ta’allaka ne da karya da kuma tona asirin gwamnati.

Aiguobarueghian ya lura cewa adadin mambobin da suka sanya hannu kan takardar ya zarce kashi biyu bisa uku da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Shugaban majalisar, Blessing Agbebaku (PDP-Owan-West), wanda ya amince da karbar takardar tsigewar, ya umurci magatakardar majalisar, Yahaya Omogbai, da ya ba da sanarwar tsige mataimakin gwamnan.

MAgbebaku ya kuma baiwa mataimakin gwamnan kwanaki bakwai domin ya mayar da martani ga sanarwar tsige shi.