Watanni 2 Malaman Furamare A Neja Suna Yajin Aiki, Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Ba Su Sulhunta Ba

Watanni 2 Malaman Furamare A Neja Suna Yajin Aiki, Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Ba Su Sulhunta Ba

 

 

Daga Awwal Umar Kontagora, Minna.

 

 

Sakamakon kin biyan kason albashin ma'aikatan ƙananan hukumomin da ya janyo rufe makarantun faramare a dukkanin ƙananan hukumomi 25 na jihar Neja,  yajin aikin da ƙungiyar malamai reshen jihar(NUT) ta kira kusan makwanni tara ke nan sama da wata biyu, hakan  ya hasala gamayyar ƙungiyar ƙwadago in da ta bijiro da wasu buƙatu ga gwamnatin jiha, kan janye biyan kason albashi saɓanin cikakken albashin ma'aikata da dokokin ƙasa ya tsara.

 

Buƙatun sun haɗa da biyan kuɗin fanshon waɗanda suka yi shekaru da barin aiki da gwamnati ta kasa biya, mayar da kuɗin asusun ma'aikata ( Cooprative) da gwamnati ta kwashe a asusun ajiyar, da tabbatar da biyan kuɗaɗen hutun ma'aikata da ake biyar gwamnati, wanda an kwashe sati ɗaya da fara yajin aikin gargaɗi na sati biyu da ya janyo rufe dukkanin ma'aikatun gwamnatin jiha har da asibitoci.

 

Da yake amsa tambayoyin manema labaru bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na gamayyar ƙungiyar ƙwadago ( NLC), Kwamred Yakubu Garba, yace ƙungiyar ta umurci ma'aikatan ƙananan hukumomi da su fara yajin aikin daga daren juma'a 4 ga watan Maris inda ma'aikatan jiha suka bi baya daren littinin 7 ga watan Maris, dan haka yau juma'a 11 ga watan nan ƙungiyar mu ta umurci dukkanin ma'aikata a matakin ƙananan hukumomi da jiha da su cigaba da wannan yajin aikin gargaɗin na sati biyu wanda idan ba mu samh daidaito da gwamnati ba mun tafi ke nan har sai gwamnati ta biya muna buƙatun mu.

 

Yajin aikin dai ya janyo tsayuwar harkokin yau da kullun da ya jefa dubban jama'a cikin matsin rayuwa musamman ruwan fanfo, kiwon lafiya da ilimi, bayan rufe makarantun faramare, ma'aikatar da ke samar da ruwan sha a jihar tayi tsayin goɗiyar Ada, da yanzu haka a wasu sassan cikin garin minna a na sayar da kurar ruwa daga naira ɗari takwas zuwa naira dubu ɗaya saboda wahalar ruwa da ake fama da shi.

 

Rahotanni dai sun tabbatar da wasu buƙatun ƙungiyar gwamnatin jiha ta amince da su amma dai har zuwa haɗa rahoton ba a kai ga cin ma matsayar janye yajin aikin ba.

 

Dakta Umar Faruƙ Abdallah, sakataren ƙungiyar limaman juma'a na jihar kuma limamin masallacin juma'ar Bosso Estate, ya nemi ƙungiyar da ta sassauta ta janye yajin aikin ganin irin halin ƙuncin da ya jefa dubban mutanen jihar musamman marasa lafiya da ba sa samun kulawar ma'aikatan jinya da likitoci.

 

Malami yace ya kamata gwamnati ta ji tsoron Allah ta saurari buƙatun ƙungiyar domin kawo ƙarshen yajin aikin. Maganar da na ke yi halin da muke ci yau na raahin zaman lafiya, da rufe makarantu ba ƙaramin koma baya zai janyo a gaba ba, domin duk kan al'ummar da ta kasa samun ilimi da kiwon lafiya za ta tsinci kan ta a wani mummunar yanayin da zai iya illata rayuwar matasa masu tasowa a gaba.

 

Zuwa yanzu dai al'ummar jihar sun zura idanu dan tunanin ko gwamnatin jiha za ta saurari koken ƙungiyar ƙwadagon dan kawo ƙarshen wannan yajin aikin.