'Yan sanda a sun tabbatar da sace dalibai 15, malamai 4 a kwalejin Zamfara

'Yan sanda a sun tabbatar da sace dalibai 15, malamai 4 a kwalejin Zamfara

'Yan sanda a sun tabbatar da sace dalibai 15, malamai 4 a kwalejin Zamfara

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

 Rundunar ‘yan sandan   jihar Zamfara ta tabbatar da hallaka wasu masu gadi  biyu da wani sifeton 'yan sanda  a lokacin da wasu da ake zargin ‘'yan bindiga ne suka kai hari a Kwalejin Aikin Noma da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura.

 Rundunar 'yan sandan ta kuma  ce  'yan bindigar sun sace dalibai 15 da malamai 4.

 Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda, sufurtanda ( SP) Mohammed Shehu, ya fitar ya ce' yan fashin suna da yawa kuma sun je Kwalejin da misalin karfe 12 na dare da nufin sace dalibai da ma'aikata da dama, amma jami'an 'yan sandan katta kwana sun yi artabu da su sosai, wadanda nan take suka karɓa kiran gaggauwa.

 Ya ce jami'an 'yan sandan da suka bi yan ta'addan cikin  daji, sun samu nasarar  kubutar da ma'aikata 3.

Ya ƙara da cewa idan an kare  yi musu tambayoyi, za  a duba lafiyarsu kafin a sake sada su  da 'yan uwan su.

 Haka zalika Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba Elkana,  ya ziyarci kwalejin, inda ya ce  'yan sanda za su yi duk abin da ya dace, don tabbatar da kubutar da ɗaliban da ma'aikatan kwalejin da aka sace.

 Kwamishinan 'yan sandan ya yi wani taron gaggawa da mahukuntan makarantar haɗi da 'yan uwan waɗan da abun ya shafa  ya gaya masu cewa 'yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, musamman sojoji, suna amfani da dabaru daban -daban na bincike don  ceto ɗalibban  cikin koshin lafiya. 

 Kwamishinan ya ci gaba da zagaye makarantar don tantance tsarin tsaro na yanzu, don ba da damar ba da ƙarin ƙarfin gwiwa game da duk wani mamayewa.

 Shugaban makarantar ya yaba da irin jajircewar  jami’an ‘yan sandan kan yadda suka tsaya kai da fata suka yi aikin da ya kamata duk da sace daliban 15 da ma’aikatan hudu.