AMBILIYAR RUWA TAYI SANADIYYAR MUTUWAR DABBOBI DA KAYAYYAKIN LANTARKI A RUKUNIN GIDAJEN INUWA DUTSE A JIGAWA

AMBILIYAR RUWA TAYI SANADIYYAR MUTUWAR DABBOBI DA KAYAYYAKIN LANTARKI A RUKUNIN GIDAJEN INUWA DUTSE A JIGAWA

 

 

Daga Ali Rabiu Ali Dutse, Jihar Jigawa.

 

 

Al'umar unguwar RUKUNIN gidajen Inuwa Dutse dake Danmasara sun koka da irin amaliyar ruwan da suka fuskanta a sakamakon ruwan da akayi Kamar da bakin kwarya a safiyar lahadi 26 ga watan yuni, 2022.

 
Shugaban kungiyar rukunin gidajen Abdullahi Hamza Usman ya koka da yanayin da suka tsinci kansu sakon makon wannan shine na farko da aka samu babbar ambaliya a bana.
 
Usman yace tun shekarar 2019 suke Kai korafin su ga gwamnati domin ta kawo musu dauki Amman haryanzu abin ya gagara.
 
Ya ce akwai lokacin da mataimakin gwamnan jihar Jigawa ya ziyar ci wajen ambaliyar a shekarar 2020 domin ganewa idon sa lamarin Don kawo dauki.
 
Abdullahi Hamza Usman ya ce anyi asarar dukiyoyi masu yawa da asarar dabbobi da kaji.
 
A nasa bangaren, wani magidanci a unguwar, Barista Hussaini Abdullahi Taura ya ce lokacin da ruwan yayi karfi sai da ya Kira 'yan kwana kwana suka kwashe masa iyalinsa daga gidan sa sakamakon ruwan yayi yawan da baza su iya fita ba.
 
Barrister yace sun dade a wannan matsalar kuma abin ya fi karfinsu a halin yanzu tunda sunyi iya bakin kokarinsu wajen kaucewa matsalar Amman abin ya gagara.
 
Shima babban limamin masallacin rukunin gidajen Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure, ya ce wannan iftila'i ne da mutanen unguwar suka tashi dashi, yace wannan zaizama kalubale da asarar rayuka idan gwamnati batayi wani abu a wannan al'amarin ba.
 
Kazaure ya yi kira ga gwamnati da mahukunta dasuyi mai yuwuwa wajen sun kawowa unguwar ta su dauki.