Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru da ke jihar kebbi Hon Bala Mohammed Isah Gajere, ya kaddamar da ayyukan jin kai a garin Zuru
Bala Gajere ya yi tattaki ne a sansanin yan gudun hijira da ke cikin garin Zuru domin duba halin da suke ciki biyo bayan hare-haren'yan ta'adda da suka rabasu da muhallan su tallafin da ya kai ga yan gudun hijira na daga cikin amincewar gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu,
Yan gudun hijira fiye da dubu 3000: ne ke zaune a karamar hukumar mulki ta Zuru na jihar kebbi kuma sun amfana da tallafin kayan abinci da sauran abubuwar more rayuwa daga Hon Bala Mohammed Isah Gajere,
A lokacin kaddamar da tallafin Hon Bala Mohammed Isah Gajere ya yi kira ga mata yan gudun hijira da su kula da karatu da kuma tarbiyyar ya'yansu,
Tallafin da Bala Gajere keyi na tallafawa marasa galihu duk da cewa al'ummomin da ke fama da hare-haren 'yan tada kayar baya yanzu suna gudanar da ayyukan noma da sauran sana'o'i don samun dorewar rayuwa,
Bala Gajere ya ce gwamnatin jihar kebbi ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta mayar da yan gudun hijira a gidajensu domin su cigaba da rayuwa kamar kowa,
Ya ce gwamnantin jihar kebbi tana bada cikakken goyon baya ga jami''an tsaro akan matakin da suke dauka na murkushe yan bindiga.
Bala Gajere ya bayyana jindadinsa da irin goyon bayan da gwamnan jihar kebbi ke baiwa wajen ganin an murkushe yan bindiga da suka addabi yankunan karkara da hare-hare.
A nasa bangare shugaban kwamitin masu kula da jindadi da walwalar yan gudun hijira na kasar Zuru kuma mataimakin shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Rabiu Garba Aiki Bedi ya sanar da cewa gwamnatin jihar kebbi na duba dukkannin hanyoyin da zata bi wajen hada kai da gwamnatin Najeriya da sauran kungiyoyin agaji domin samar da hanyar da za abi.
Yayin da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa Rabiu Garba Aiki Bedi ya sanar da cewa gwamnatin jihar na Kokari akan sha'anin da ya shafi tsaron yankunan da abin yake shafa kuma ya bada tabbacin cewa komai zai yi daidai yan gudun hijiran sun fito ne daga garuruwan Sakaba Danko Wasagu da jihar Neja mai makwantaka da jihar kebbi.
A jawabin godiya yan gudun hijiran sun godewa Hon Bala Mohammed Isah Gajere da assasa wannan tallafin inda suka roki Allah ya saka da mafifincin alkhairi.