Zanga-zanga: Mun kama sojan da ya harbe yaro ɗan 16 a Zaria - Rundunar Sojin Ƙasa
Rundunar Sojin Najeriya ta tsare jami'inta da ya kashe wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed a yayin zanga-zanga a garin Samaru na Zaria a jihar Kaduna ranar Talata.
Bayanin hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a Abuja.
Nwachukwu ya ce sojojin sun samu kira kan cewa ɓata gari sun taru a Samaru ta Zaria suna kone taya a kan hanya tare da jifan jami'an tsaro.
Ya ce sojoji sun isa wurin domin tarwatsa matasan tare da tabbatar da an bi dokar kulle da gwamnatin jihar ta sanya.
"Yayin da sojoji suka isa wurin, sai ɓata gari suka yi yunkurin farmakarsu abinda yasa sojoji suka fara harbi sama don gargadi wanda hakan ya kai ga rasuwar Ismail Mohammed mai shekaru 16.
" Sojan da yayi harbin an kama shi, yana amsa tambayoyi a yanzu haka", inji shi.
Nwachukwu ya ce babban hafsan sojin kasa, Lt.Gen. Taoreed Lagbaja ya kadu da faruwar lamarin.
Sannan ya ce an tura tawaga domin yin ta'aziyya ga iyalan mamacin.
managarciya