Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari---Sarki Sanusi

Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari---Sarki Sanusi

Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi kuma mataimakin shugaban hukumar bunkasa saka hannun jari na Kaduna, ya ce yana tausayin wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda tattalin arziki ta tabarbare.

Sanusi, wanda kuma shine Khalifa na darijar Tijanniya a Najeriya, ya furta hakan ne a ranar Asabar a Kaduna yayin da ya ke jin jawabi ga yan siyasa a wurin taron da aka yi wa lakabi da "Gina Kwakwaran Tattalin Arziki". 
Sarkin Kanon na 14 ya ce tattalin arzikin kasar ya dogara ne ga man fetur da iskar gas kuma cire tallafi yana kara gurgunta tattalin arzikin, rahoton The Punch. Ya koka kan yadda Najeriya ta dogara da ciyo bashi kuma wasu tsiraru da ke mulki a kasar ke azurta kansu su zama attajirai cikin dare daya. Ya ce idan aka cigaba da haka rashin tsaro zai iya tabarbarewa kasar ta zama tamkar Mali da Burkina Faso.