'Mun kashe Naira Biliyan 12 Wajen Sayo Kayan Asibitin Koyarwa Ta Jami'ar Sakkwato'------Gwamnatin Tambuwal

'Mun kashe Naira Biliyan 12 Wajen Sayo Kayan Asibitin Koyarwa Ta Jami'ar Sakkwato'------Gwamnatin Tambuwal

Daga Jabir Ridwan.

Gwamnatin Jahar Sakkwato ta bayyana cewa a amko mai zuwa ne zaa soma sanya kayan aiki ga asibitin koyarwa ta jamiar Jahar Sakkwato.

Kwamishinan lafiya na Jahar Sakkwato Dr Ali Mohammad Inname, ne ya sanarda haka a yayin gudanarda wani taro da wakilan kamfaninda aka baiwa aikin Thomat Company Nigeria Ltd, taronda ya gudana a harabar asibitin.

Dr. Muhammad Ali Inname, yace wannan ya biyo bayan amincewar gwamna Aminu Waziri Tambuwal, na cefano kayakin tareda sanya su, kudinda suka kai kimanin naira Biliyan 12.

A cewar sa, zaa gudanarda aikin ne rukuni-rukuni, kasancewar aikin yanada yawa.

Dr, Inname ya jaddada cewa zaa soma sanya kayan aikin ne a sashen kulawa da mata da kananan yara, da kuma dakunan masu gata wato Amenity, da sauran muhimman wurare.

Kwamishinan hakama ya bayyana fatanda yake dashi na ganin asibitin ta soma aiki farkon watan janairun badi.

Daga karshe ya umurci kamfanin da aka baiwa kwangilar aikin daya hanzarta kamala aikin cikin lokaci.
  
Wannan na kunshe ne cikin wani bayani mai dauke dasa hannun jamiin hulda da jamaa na maaikatar lafiya ta jaha Nura Bello Maikwanci.