Wata Jigo a Jam’iyar APC Hajiya 'Yar Halima Tudun Wada ta fice daga jam’iyar APC zuwa Jam’iyar PDP a Sakkwato

Wata Jigo a Jam’iyar APC Hajiya 'Yar Halima Tudun Wada ta fice daga jam’iyar APC zuwa Jam’iyar PDP a Sakkwato

 

Ta sanar da ficewarta a wani taron da Uwargidan Malam Saidu Umar ta shirya mata a Cibiyar horar da matasa ta youth center dake nan Sokoto.

 

Hajiya Yar Halima Tudunwada tace ta yanke hukuncin barin Jam’iyar APC saboda rashin alkibilar siyasa a Jam’iyar da kuma siyasar ubandgida tareda rashin saka mata cikin harkokin siyasa a Jam’iyar.
 
Hakama tace akwai rashin kwarewa da ingancin dan takara a Jam’iyar ta APC, inda ta kara dacewa gwamnatin APC mataki na kasa ta kasa magance matsalar tsaro da ya addabi kasar nan shiyasa taga batada zabi illa ta chanza sheka da ita da magoya bayanta.
 
Hajiya Yar Halima tabada tabbacin yin aiki tukuru domin Samun nasarar Malam Ubandoma a zabe mai zuwa.

 
Da take karbar wadda ta chanza sheka Uwargidan Dantakarar Gwamna na jam’iyar PDP Hajiya Hindatu Saidu Umar ta bayyana cewa Hajiya Yar Halima tayi kyakyawar tunani da lokacin da ya dace.
 
Hajiya Hindatu ta kara da cewa idan Malam Ubandoma yayi nasara a zabe mai zuwa zai tabbatar da an ba mata kyakyawar wakilci a gwamnatinsa.
 
Hajiya Hindatu tayi alkawalin yin aiki tareda Hajiya Yar Halima domin samun nasarar Jam’iyar PDP a kowane mataki.

 
Sauran matan da sukayi magana a wurin sun hada da matar shugaban karamar hukumar Sokoto ta Kudu Hajiya Zainab Faruku Sayudi da kuma Shugaban mata ta PDP na karamar hukumar Hajiya Rabiatu Hassan.