Tinubu Ya Nada Gwamna Masari da Tsohon Gwamnan Sokoto a Muhimmin Muƙaman Kamfe 

Tinubu Ya Nada Gwamna Masari da Tsohon Gwamnan Sokoto a Muhimmin Muƙaman Kamfe 

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya naɗa gwamna Aminu Masari na Katsina a matsayin mashawarci na musamman kan jagoranci na tawagar kamfe. Premium Times tace Tinubu ya kuma naɗa tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma Sanata mai ci, Aliyu Wamakko a matsayin babban mashawarci kan ayyuka na musamman. 
A wasikun naɗin da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja kuma ɗauke da sa hannun Tinubu, dukka jiga-jigan biyu zasu yi aiki ne a tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa. 
Wasikun sun yi bayanin cewa Masari da Wamakko sun samu nasarori masu ban sha'awa a siyasa kuma shugabanni ne abin koyi a matsayin gwamna da Sanata, sun dace da muƙaman.
"Ta wannan takarda muna sanar da kai cewa an naɗa ka mai ba da shawari na musamman kan harkokin shugabanci da gwamnati a tawagar kamfen Tinubu/Shettima." 
"Wannan naɗi ya dace kuma a kan lokaci duba da nasarorinka a siyasa da kuma shugabanci abin koyi da kake aiwatarwa a matsayin gwamna da kuma mamban jam'iyya." 
"Mun ji daɗin jawo ka cikin tawagar kamfe kuma mun san zaka yi duk me yuwuwa don sauke nauyin da aka dora maka dai-dai gwargwado." 
A wasiƙar, Tinubu, ya nuna kwarin guiwar cewa Masari zai taimaka wajen gudanar da kamfe mai tsafta da zai kai APC ga nasara a zaɓen 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.