Sifeto-Janar Na 'Yan Sanda Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro A Makarantu

Sifeto-Janar Na 'Yan Sanda Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro A Makarantu
 
Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bada umarnin kai jami’an tsaro zuwa makarantu, cibiyoyin lafiya da sauran gurare masu mahimmanci a fadin kasar nan.
 
Bayanin haka na dauke cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Olumuyiwa, ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.
 
Sanarwar tace, Baba ya kuma bada umarnin yin sintiri da binkice akai akai, domin dakile duk wani shiri na ta’addanci a kasar nan.
 
Sannan kuma ya ja kunnen jami’an na ƴan sanda da su nuna kwarewa, jajircewa da kuma bin dokokin aiki ya yin gudanar da aikin su a fadin kasa baki daya.