HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 21

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta 21

HAƊIN ALLAH

   
       

    


            Page 21

Na duƙa na ɗauki wayar na shige ɗaki, kuɗin na ƙirga naga sun kama dubu goma sha takwas, nayi murmushi na adana abuna na miƙe cike da ƙwarin gwiwa na ɗora sanwar taliya, cikin lokaci kaɗan na gama, na zuba a tire na zauna kenan zan ci sai ga ƙanina da gudun masifa yana ta shassheka ya faɗi gabana yace, "Mamarmu tace, duk abin da kike ki yi maza ki je tana nemanki yanzu-yanzu." 
Gabana ya faɗi na kalle shi nace, "Bata da lafiya ne?" Ya girgiza kai sai kuma yace, "Lafiyarta lau Babansu Haidar ne ya je da gudu yace kin ɗauki wuƙa za ki kashe shi." Ni abin dariya ma ya ban, don haka sai na gyara zama na ce, "Idan zaka ci abinci, bisimillah ka ji, idan muka gama mun je kiran ba na gaggawa bane ashe."  Ya zauna kuwa na zuba mai, muna ci ina tambayarshi abin da Abban Haidar ya ce da yaje. Yana dariya ya ce, "Yo yana shigowa sai ganinsa mu kai kanmu yana ta nishi yana kallon bayansa, shi ne Mamarmu tace mai lafiya kuwa? Ya ce "Wallahi Jiddah ce ta fiddo wuƙa zata kashe Ni, shi ne na rugo nan, don Allah ki bata haƙuri kar da ta kashe Ni."
Mamarmu ta zabura tana Salati tace, "To ita kam me ke faruwa da ita ne? Kanta lafiya kuwa, anya tana cikin hayyacinta kuwa?"  Ya zauna yana cewa a ba shi ruwa masu sanyi don Allah. Shi ne fa tace na rugo da gudu na kira mata ke.

Sai da muka gama cin abincin na amso yarana sannan na tasa ƙanina gaba, muka nufi gun Mamana ina tafe ina lissafin yadda za mu da Mama idan na isa, nasanta bata da son rigima kwata-kwata magana kanta bata dameta ba, nasan tana can ta kasa tsaye ta kasa zaune Yau ta ji zan yi kisan kai.

Muna shiga kau na iske ta tsaye tayi zugudum alamar tunani take, tana ganina tai ajiyar zuciya ta shige ɗakinta na bita. Tun kafin in zauna ta fara cewa, "Wane irin mugun labari ne nake ji ya fito daga gareki ɗiyar nan? Kisan kai fa nake samun labarin za ki aikata? Anya kuwa kin san darajar aure kin san wane ne miji da darajarsa? Shin kina san ki gama da duniya lahiya kuwa ɗiyar nan?" Ai sai Mama ta fashe da kuka abin da ya tada min hankali kenan, domin ba abin da na tsana irin naga Mama ta sauya fuska ko alamar damuwa a tare da ita, sai nima na kama kukan na kasa gaya mata abin da ya faru. Sai da muka gama kukanmu sannan Mama tai ta min nasiha taban shawarar na dinga shan ruwan alwala idan na rage ta sallar la'asar.

Ni dai na samu naita bata haƙuri har muka rabu lafiya na kama hanya na koma gida ina jiran Abban Haidar ya zo naga da me zai zo kuma. Wai nice nace zan kashe shi! Abin yaban mamaki ba ɗan kaɗan ba, tabbas na yarda Abban Haidar zai iya shiga tsakanina da Mama don haka ya zama tilas na san matsaya ta da shi, don ba zan lamunci ya dinga zuwa yana tada ma tsohuwata hankali ba. 

Da dare na leƙa gidan Maman Khairat na gaya mata abin da ya faru Yau, da yadda mu kai da yarinyar da Abban Haidar yaba kayana da zuwansa gun Mamana da yadda ya je ya yi min sharri gun Mama zan kashe shi.

Itama dai faɗa tai min kan bai kamata ba, da na bar mata kawai na kwashe kayana daga gidan shike nan, ai sai ya gani sannan zai ɗauka, idan ban aje ba ya gani ai ba zai ɗauka ba.

Wajen tara na dare na bar Haidar nan gidan ya ɗauki su Afnah na nufi gida hankalina kwance.

Sai can cikin dare naji alamar shigowar Abban Haidar kamar naje nayi mai magana sai kuma na fasa, kamar na ɗauki wayarsa na ba shi sai kuma na tuna wayata huɗu yana saidawa daga aro, wata ma ɗauka kawai yake sai dai na fahimci ya saida da kaina ba dai ya gayamin ya saida ba, haka waya uku yana cinyewa ta Mama don haka don naci wannan ba wata tsiya bace, cikin wanda ya ci nawa ne na amshi guda, ko da na gama wannan tunanin sai na ɗauko wayar na zare sim card ɗin na tura gefen kujera wayar kuma na adana ta cikin jakar hannuna.

Bayan na gama sallar asuba na koma na kwanta naji mutum kan kaina yana magana, Ni kuma daman nace idan dai ba kiran sunana ya yi ba ko yace Maman Afnah ko Afnan ba zan amsa ba don ya shekara kirana da Ke.  Komi ya gani sai ya ɗan bubbuga ƙafa ta na buɗe idona na watsa mai su, nace "Lafiya Abban Haidar?" Cikin maganar hanci ya ce, "Ina wayata? Kamar nan na yada ta jiya."  Na tashi zaune ina murje idona nace, "Wace wayar kuma Abban Haidar? Ni ba wanda ya kawo min ajiyar wayarka nan gidan gaskiya."  Ya ɗan tsura min ido kamar yana son karantar wani abu kan fuskata sai kuma ya ja tsaki ya juya ɗaki.

Na taɓe bakina na gyara kwanciya ta, nace a raina kai dai ka sani amma waya da kuɗi sun zo kenan sai dai wasu.

Bayan na gama gyara gidana nayi wanka na yiwa yara na wanke kayan da na cire masu don na saba da yadda tsohuwar dake dafa min ruwan wanka take tana gama masu wanka take wanke kayansu, nima sai na ɗauki halin ina gama masu wanka nake wanke kayansu.

Hatta karin kallo na gama, na shirya tsab ina karanta wani littafi (ADON DAWA) na Jamila Umar Tanko, sosai labarin soyayyar Aunty Madina da Abba ya tsaya min a zuciya, ko shakka babu irin soyayyar da nakeafarkin samu kenan a rayuwata, amma ina zan masu mai yi mun ita? Duk da cewa har zuwa yanzu ban cire rai da samun irin wannan soyayyar ba, amma na rasa ta ina zata zo min, waye zai nuna min ita ? A wace duniyar za mu haɗu? Duk ban sani ba, amma nasan dai ba zan iya barin gidan Abban Haidar ba, saboda ba inda zan je idan na bar gidan, amma ina addu'ar Allah Ya azurta Ni da samun soyayyar da nake mafarki ko da ta yini guda ce a wajen Abban Haidar... Sallamar da na ji ce ta katse min tunanina na tashi duk da nasan maigidan na nan na nufi ƙofar gidan don ganin mai sallamar saboda tunda na fara sana'a mutane na zuwa amsar atamfofi da shadda wajena bashi sai ƙarshen wata su biyani, shi yasa Abban Haidar idan za a shekara sallama bai amsawa balle ya fita.

Ina zuwa kau na iske Baban yarinyar jiya, na duƙa na gaida shi, domin tsoho ne, ya dube ni ya sadda kansa ƙasa ya ce, "Yarinya na zo ne na kawo maki kayanki, na kuma baki haƙuri kan abin da ya faru don Allah ki yi haƙuri yaran yanzu ka haife su ne baka haifi hakinsu ba." Na miƙa hannu na amshi kayana na duba naga komai na ciki nace ina zuwa.

Komawa nayi ɗaki na ɗauki kuɗin na ƙirga dubu takwas na ƙirga huɗu sai kuma na tuna ba lallai bane ba idan ya je yaba matar kuɗinta don haka sai na aje na matar na fita na ba shi kuɗin shi nace "Ƙirga Baba." Ya gama ƙirgawa ya ce, "Tabbas sun cika haka na baki su." Nace to madalla, amma don Allah Baba idan kun ɗorawa yaranku talla ku dinga ankarewa da abin da suke idan sun zo birni tallar don gudun lalacewa.

Ya girgiza kai ya ce, "Ke dai bari ɗiyata ai Hinde ta ja wa kanta domin jiya muna komawa gida sai ga aike daga gidan angwayenta wai a basu kayan aurensu sun fasa, sun samu labarin abin da ya faru."

Naji ba daɗi amma kuma ya na iya, don haka nace, "To Baba me zai hana ku ce shi maigidan nan (Abban Haidar) ya fito a maida auren kansa?"  Ya yi murmushi irin nasu na manya ya ce, "Ai hakan ba zai yiyu ba, saboda kowa nasan ya kai nashi gidan kirki ɗiyata ke dai ki ta haƙuri da addu'a." Ya barni tsaye ina jinjina maganarsa,

Abban Haidar na iske zaune kan kujera ya dubeni fuska ba walwala ya ce, "Ai sai ki ban kuɗina yanzu ko? Tunda an kawo maki kayanki, bayan rashin mutunci da rashin kunya ma me ye abin rufe masu yarinya daga kawai kin ji labarin an bata kaya sai kace ke kaɗai ce mai kaya a garin nan." 

Yanzu Ni kaina nasan nafi Abban Haidar miskilanci don haka duk maganar da yake ƙala ban ce ba, ko inda yake ma ban kalla ba, ƙoƙarina guda shi ne na goya Afnah na saɓa Afnan na bar gidan don ban san muna zama ko kusa da juna.

Gabanshi na fiddo da sauran kayana na ƙirga na tattara su na ɗauki sabon kwaɗon dana siyo guda biyu na fitar da makullan na raba su biyu na aje mai rabi na fice da rabin na sungumi kayana  na fitar waje na kai gidan Binta sannan na dawo na ɗauki Afnan duk yana yadda na barshi.

Alhamdulillah! Sana'a ta amshe ni domin yanzu har kayan kicin nake siyowa ina saidawa, na koma ba abin da ban saidawa kuma ina samu ba laifi, don haka ba wanda zai ganni yace ina fuskantar matsala a gidan aurena. 

Sai dai zuwa lokacin tsakanina da Abban Haidar sai ido domin na gaji da yadda yake kawo mata cikin gidan da zarar na fita, tabbas idan zan dawo da wuri sai na iske shi da wata hakan na ƙara jefa min wutar tsanarsa a raina amma ba yanda zan a haka dai nake cijewa bayan lokaci-lokaci ina ba shi haƙƙinsa idan ya nema. 

Lokacin dana yaye su Afnah sai kasuwa ta fara ja baya domin mutane duk sun amshi kaya ba kuɗi wasu kuma idan an kawo aka iske Abban Haidar bai ban sai ya kashe,sai dai idan naje bin bashin ace an kawo min suna hannun maigidana, idan na zo nayi mai magana bai tankawa shike nan kuɗin sun wuce Ni ba zai taɓa ban su ba. 

Dana gane sai ya kasance duk wanda zan ba kayana sai na gaya mai idan zai ban kuɗi hannu da hannu zai ban kar aba Abban Haidar kuɗina. Mutane da yake ba a iya masu nan wasu su kaita gulmata wai ban iya ba shi ko sisi ban iya sakar ma sa dukiyata yana mijina kaina kawai na sani sai yarana. Ni dai idan ana gaya min dariya kawai nake domin nasan shi yasan ina yi ma shi yadda ya kamata bai taɓa ɗaukar shadda ko yadi ya biya kuɗin ba, haka duk wanda ya kawo ya sai kaya shi zai je ya amshi kuɗin bai ban su.

Maganar abinci kuwa dama ya daina kawowa sai dai idan ya iske na yi ya ɗauka ya ci har ya fitar majalisa.

Ganin kuɗin kayana sun yi ƙasa sosai sai na je gun Mama mu kai shawarar na sari hatsi da kuɗin na aje idan lokacin saidawa ya yi sai na fitar in samu kuɗin cigaba da sana'ata. Haka kuwa akai na sari waken suya da kuɗin duka na adana su a gidan Mama saboda ban san a samu matsala don sau huɗu ina siyen tumaki yana saida min hatta kaji bai barinsu saidawa yake don haka na aje su can bakina alaikum.

Ban san ya akai ba ashe Abban Haidar ya je gun Mama ya ce mata, ta ba shi rancen kuɗi zai siyi takin noma ya samu gonar da zai noma. Ita kuma tace mai bata da kuɗi amma ga waken matarka nan tunda duk abin ƙaruwa ne ai ka ɗauki buhu biyu ka saida ya isheka sai ka sai takin yafi ace a je wani waje neman rance. Nan da nan kuwa ya ɗauki buhu biyu ya je ya siyar ya kama bushasha da kuɗin ni dai naga sai ya zo da lemu yana sha, ko ya zo da tsire yana ci ga fura mai madara yana zuwa da ita kullum, abin takaicin bai ba ko yaran dake kallonsa haka zai zauna ya cinye ko ma miye ya shigo da shi, sai dai duk yaron da ya kalle shi sai ya zage shi.

Bayan wani lokaci kuma ya haɗa baki da wani abokinsa ya je ya iske Mamarmu ya ce mata, ga Deeni can an rufe kan kuɗi Naira dubu arba'in ya ranta ne ya kai ma wani mutum da yace zai samar ma shi aiki ashe ɗan damfara ne, nan dai Mama tace a ida kwashe waken a saida a je a biya kuɗin a fito da shi, duk ba abin da na sani sai da na je da niyyar ɗaukar wake a saida sannan take gayamin yadda akai, tace ai ta ɗauka ya gayamin komai ai shi yasa ban mata maganar ba tunda na sani.

Kasa magana nayi kawai nace Allah Ya kyauta na dawo gida na rasa abin da ke min daɗi, ga shi na kasa daina tuna abin a raina kuma na kasa yi mai maganar sai dai na zauna nayi ta tunanin banza a raina.

Haka na tafi rayuwa tai min zafi na koma tamkar ban taɓa kama kuɗi ba, komai ya tsaya min wahala ta dawo sabuwa dal ga yara sai wanda ya ga Allah yaga Annabi kawai ke taimaka min. Don ma Maman Khairat na tsaye kaina da yarana yasa nake samun sauƙin wasu abubuwan, amma duk da haka sai da takai ga hatta sabulun wanki dana wanka ya gagareni. Ganin wahalar tai yawa Maman Khairat tai ma mijinta magana ya samar min aikin polio duk wata ana biyana kuɗin aikin, duk da ba cikin gari nake zuwa aikin ba ban damu ba murna nake domin duk sanda mu kai aikin ana ban kudin abinci dana mota  dasu zan sai sabulun wanki dana wanka har na saima Mama itama a ciki. Cikin ikon Allah sai na fara samun sauƙin wahalar rayuwa, sai abin da ba a rasa ba.

Duk da haka na kasa manta abin da Deeni da Safiya su kai min, ko da yaushe na tuna da abin sai nayi kuka haka sai naji tsanar Deeni fiye da baya a raina. Ban sani ba ko hakan yasa ma baki ɗaya sha'awata ta ɗauke oho, Ni dai nasan ba abin da na tsana a rayuwata irin daren da Deeni zai neme Ni sai naji kamar na kashe kaina na huta sam ban jin daɗin abin har ya yi ya gama ina hawaye wanda na lura shi baima san ina yi ba.

Lokacin ne hawan jini ya takura min sosai, ga ba waya tsakaninmu da Hajjo da Uncle Salim tunda na saida wayata na ajiye sim card ɗin Deeni ya ɗauke shi daga aro yace min ya faɗi, itama Mama ba waya gunta ya je ya amsa daga aro bai maida mata ba, don haka ban da labarinsu basu da labarina daman jira nake na saida wajen na haɗa kuɗaɗen na koma Kano sarin kaya sai naje can to ga yadda akai da waken babu shi ba kuɗin duk Deeni ya salwantar da shi.

Duk lokacin da ciwon zai kwantar da ni sai dai mutanen unguwa su haɗa kuɗi masallaci su sai min magani ko a kai Ni asibiti amma ba ruwan Deeni da ciwona ko sannu bai iya yi min idan ban lafiya.
Sai ta kai ma idan an siyo min maganin yana ɗauka ya je ya saida saboda suna da tsada maganin hawan jini, ƙarshe suma ƴan unguwar suka watsar da lamarina ko ban lafiya iyaka ai min sannu kawai sai masu dama ke aiko min da abinci idan sun girka da rana ko dare.

Ina a haka na daure na shiga adashe na kuɗi Naira dubu biyar duk wata, saboda duk wata idan mu kai polio ana bamu dubu shida da ɗari shida, ganin halin da nake ciki ne aka ban kwasar farko -farko don in samu abin da zan tsaya da ƙafafuna, ranar da aka kawo min kuɗin Deeni na kwance cikin ɗaki ashe yana ji na ƙirga kuɗi Naira dubu tamanin cif na zari dubu biyu nace ma Uwar adashen ga shi ladar gurbi tace Wallahi ba zata amsa ba, nayi-nayi da ita taƙi amsa nayi godiya na tashi na rakata.

Na dawo ina tunanin me zan da kuɗin wanda zan samu, har dai dare ban samu matsaya ba, don haka nace gobe zan je da su gun Mama mu ji wace sana'a zan fara da su.

Ban saba makara ba sallar asuba amma Yau sai na makara, na tashi da sauri nayi alwala na fara sallah kenan naga Deeni ya fice da sauri rataye da jaka a kafaɗarsa, sai da na gama sallah nayi lazumi na sannan na fita tsakar gida na gama shara da wanke-wanke na dawo na gyara ɗakin na kammala komai nace bari na ɗauko kuɗin na ƙirga sai na ɗauki dubu na siyo fulawa nayi mana wainar fulawa, kuɗi suka ce ɗauke mu inda kika aje mu.
Abu kamar wasa na duba kuɗi basu ba labarinsu kaf ɗakin, ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, tabbas Deeni ne ya kwashe kuɗin ya fice tunda asuba.
Cikin sauri na zari hijabina na rufe gidan yarana na barci na nufi gidansu Deeni ko zan iske shi ya je kalaci don can yake zuwa duk safiya yana karyawa mu ko oho.

Ina zuwa muka gaisa da mutan gidan na tambaye su ko Abban Haidar ya zo, suka ce ya zo ya yi bankwana wai ya tafi yawon duniya na wasu kwanaki.

Juyowa kawai nayi na koma gida, ina jin  ya zama tilas na bar Uwata nabar yarana nima na bishi yawon duniyar.
Ina kuka ina haɗa kayana na gama na ƙulle a zani na dubi yarana nai masu kallon ƙarshe na fice daga gidan.


To masu karatu ko ina Jiddah zata je?
Ina Deeni ya tafi da kuɗin Jiddah?


Taku a kullum Haupha!!!!