Kotun Zaben Gwamnan Jihar Sokoto Za Ta Yanke Hukunci a Ranar Asabar 

Kotun Zaben Gwamnan Jihar Sokoto Za Ta Yanke Hukunci a Ranar Asabar 

 

Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Sokoto ta sanya ranar 30 ga Satumban 2023, a matsayin ranar da za ta bayyana hukuncin da ta yanke kan ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen gwamna Ahmed Aliyu.

 Hakan na zuwa ne ne bayan kotun ta tanadi hukuncinta a watan Agusta kan ƙarar da Sa’idu Umar na jam'iyyar PDP ya shigar a kan gwamna Aliyu da mataimakinsa, Idris Gobir, cewar rahoton PM News. 
Mai shari'a Haruna Mshelia, shugaban kotun, ya tanadi hukuncinsa bayan ɓangarorin biyu sun samu damar gabatar da bayanansu na ƙarshe a gaban kotun. Ya sanar da cewa za a sanar da ranar yanke hukunci ga ɓangarorin a watan Satumba. 
Ƙarar da Sa'idu Umar ya shigar dai tana ƙalubalantar nasarar gwamna Aliyu wanda ya yi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da mataimakinsa Gobir. Umar ya yi zargin cewa Aliyu bai cika sharuɗɗan cancanta tsayawa takara ba, ya kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris. 
Wata sanarwa daga sakataren kotun ƙararrakin zaɓen, Sunday Martins, ta tabbatar da cewa za a yanke hukunci kan ƙarar mai lamba EPT/SK/GOV/01/2023 ranar Asabar 30 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 9:00 na safe.