Matsalar Tattalin Arziki:Atiku yana so Tinubu ya yi koyi da Shugaban Kasar Argentina 

Matsalar Tattalin Arziki:Atiku yana so Tinubu ya yi koyi da Shugaban Kasar Argentina 

Atiku Abubakar wanda ya rikewa PDP tuta a zaben shugaban kasa na 2023, ya sake yin magana a kan tattalin arzikin Najeriya. Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da wani dogon sako zuwa ga Bola Ahmed Tinubu a dandalin X, ya ba gwamnatin tarayya shawarwari. 

‘Dan takaran kuma babban jigo na jam’iyyar PDP ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu tayi koyi da salon shugaba Javier Milei a Argentina.
Atiku ya kawo mafita ne ganin Najeriya ta shiga kunci da matsin lambar tattalin arziki.
Jagoran adawar yake cewa kasashen Najeriya da Argentina sun samu kansu a mummunan yanayi, kowa ya kawo hanyar gyara. Halin da Javier Milei ya tsinci kasar Argentina, a cewar Wazirin Adamawa ya fi muni a kan yadda Muhammadu Buhari ya mika mulki. Daga kalamansa a X, Atiku yana ganin idan Tinubu ya yi koyi da gwamnatin Milei, tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa, a samu arziki. 
Zargin ‘yan adawa ko daura laifi ga magabatansa ba mafita ba ne, Atiku ya fadawa gwamnati babu ruwan ‘yan kasuwa da siyasar gida. 
"Matsalolin Argentina na kama da Najeriya – hauhawar farashin kaya, talauci da tulin bashi, Milei yana shiga ofis, ya rage facaka."