Mashawarci Na Musamman Ga Tambuwal Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
Mai baiwa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Shawara kan Sokoto Marshall jami'an tsaro mallakar jiha Alhaji Bello Malami Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyar PDP zuwa APC.
Malami ya bayyana cewa ya shiga jam'iyar APC ne saboda yanda ta samu karbuwa a jiha.
Jagoran jam'iyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko tare da ministan harkokin 'yan sandan Nijeriya Muhammad Maigari Dingyadi ne suka karbe shi a gidansa dake Gawon Nama a ranar jumu'a data gabata.
Malami Tambuwal ya sha alwashin aiki tukuru don ganin APC ta samu nasara a zabe mai zuwa a Sakkwato da Nijeriya baki daya.
Dan takarar gwamna a jam'iyar APC Ahmad Aliyu ya ce mai baiwa Gwamna shawarar ya dawo gidansu ne bayan ya tafi rangadi na dan lokaci.
"ka dawo in da ake ganin girma da mutuncinka. Ka sani jam'iyarmu mun dauki kowa abu guda ne ana tafiya cikin mutuntawa," a cewarsa.
managarciya