Wamakko Ga Gwamnonin Nijeriya: Ku jingine Maganar 2023 Ku Fuskanci Halin da Ƙasar Ke Ciki

Tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga gwamnonin Nijeriya su mayar da hankali kan kalubalen da kasar ke fuskanta bisa ga su karkata kansu a maganar  zaben shugaban kasa a 2023.

Wamakko Ga Gwamnonin Nijeriya: Ku jingine Maganar 2023 Ku Fuskanci Halin da Ƙasar Ke Ciki
Sanata Aliyu Wamakko

Sanata Wamakko ya ce wannan tirka-tirka da ke tsakanin gwamnonin Arewa da Kudu kan wane yanki ne zai karbi shugaban kasa a zaben 2023 abu ne da zai kawar da kai ga halin da kasar ke fuskanta.

"Tsayin daka da cimma matsayar gwamnonin Kudu kan sai an ba su shugabanci a 2023, su kuma gwamnonin Arewa suka mayar musu martani, wadannan abubuwa ne da suka zo da ba za ta kwarai", a ceawar Wamakko a cikin wani bayani nasa.

A bayanin da Daily Trust ta wallafa  ya yi tir da dokar da gwamnonin Kudancin Nijeriya suka yi na hana yawon kiyo a fili  wannan a matsayin abu ne na  tauye hakkin dan kasa a damar da kundin tsarin mulki ya  ba shi na ya tafi ko ya rayu in da duk yake so a cikin kasarsa ta haihuwa. 

Wamakko ya ce a kare rantsuwar da suka yi za a yi tsammanin hada kan kasa ba shigo da abubuwan rabuwar kai ba, a bayanin nasa.