Wasu ministoci a gwamnatin Buhari na shirin komawa SDP

Wasu ministoci a gwamnatin Buhari na shirin komawa SDP
Akwai alamu masu karfi da ke nuni da cewa wasu tsoffin ministocin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari za su koma jam’iyyar SDP.
Wani sanata a Majalisar Dokoki ta tara, wanda ya yi magana da Saturday PUNCH bisa sirri, ya ce aƙalla tsofaffin ministoci 10 daga gwamnatin Buhari na shirin komawa SDP.
“Abin da suke jira shi ne kammala tsari da shugabancin jam’iyyar a jihohinsu,” in ji majiyar.
Wakilan jaridar The Punch sun rawaito bayanai cewa manyan magoya bayan Buhari a wannan sauyi sun haɗa da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Adamu; tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan.
Daya daga cikin aminan Buhari kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Litinin ya sauya sheka zuwa SDP. Ya bayyana cewa dalilin yanke wannan shawara shi ne rashin daidaituwa tsakanin manufofinsa na kashin kansa da tafiyar jam’iyyar APC a halin yanzu.