Jagorancin Tambuwal A Kungiyar Gwamnonin PDP Abin Yabawa Ne---Sarkin Samarin Yabo
Jagorancin Ƙungiyar Gwamnonin PDP ƙarƙashin jagoranchin Rt. Honarabul Aminu Waziri Tambuwal CFR. ((Matawallen Sokoto) abin yabawa ne.
Alhaji Atiku sarkin samarin Yabo Wanda shi ne shugaban matasan jam'iyyar PDP na kudancin jihar sokoto, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wata tattaunawar da yayi da manema labarai.
Atiku Sarkin Samarin Yabo, Ya ce taron zaɓar shugabanni da jam'iyyar PDP ta gudanar samun yinsa, cikin tsanaki wannnan ya samu ne akan sahihin jagorancin gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal zaɓɓen gwamnan jahar Sakkwato.
Atiku ya bayyana cewa Gwamna Tambuwal shi ne jagoran dandalin gwamnoni, kyakykyawan jagorancinsa ya haifar da samun nasarar yin wannan taron lami lafiya aka kuma watse lafiya.
Sarkin Samarin, matashin dan siyasa basarake ya kara da cewa jagorancin Aminu waziri Tambuwal na fito da hanyoyi, hadakan jam'iya,matakin ƙasa,
da fitowa da dubaru kakala, naganin an sami sulhu cikin jam'iya.
Hakan ya nuna cewa,idan jam'iyar PDP tasami irinsa a matsayin dan takara, tabbas Yana iya mulkin wannan kasar ta Nijeriya ba tare da samun matsaloli ba.
Shugaban matasan na jamiyyar PDP Kuma ya jinjinawa Dandalin gwamnoni da Kuma shugaban kwamitin tsare tsare karkashin jagorancin Ahmadu Umaru Fintiri gwamnan jihar Adamawa.
Shugaban matasan jam'iyyar PDP na kudancin Sakkwato ya ce samun nasarar wannan taron na kasa yanuna cewa inshaa Allahu jam'iyyar PDP ce wadda zata yi nasara a zabukkan dake tafe a shekarar 2023.
Ya Kuma Yabawa matasa kan irin Yanda suka nuna kokarinsu a wajen wannan taron musamman lokacin da ake gudanar da shi, batare da yin bangar shiyasa ba, ko nuna halin rashin sani. Sarkin samarin yayi Adduar
Allah Yakarawa Mai girma gwamna Tambuwal jagora akan dukkanin lamurransa Hadi da shugabannin Wannan jam'iyyar Mai Albarka.
Idan baa manta ba, ranar Assabar da ta gaba ne jamiyyar PDP mai adawa alasa,kana mai mulkj a jihar Sokoto ta gudanar da taron ta a birnin tarayya Abuja,taron da jamiyar ta bayyana samun yin sa cikin nasara, inda masu sharhi kan lamurran yau da kullun da siyasa suka yabawa yadda aka zabo matashi ya jagoranchi matsan jamiyyar a matakin kasa