Buhari Da Gwamnonin APC Za Su Yi Zama Kan Babban Taron Jam'iyya

Buhari Da Gwamnonin APC Za Su Yi Zama Kan Babban Taron Jam'iyya

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin APC za su yi zama a ranar Talata kan su samar da matsaya a babban taron jam'iyarsu domin cigaban APC.

Shugaban kasa ya dage taron da aka shirya gudanarwa a satin da yagabata tare da gwamnonin kan tafiyar da ta kama shi a kasar Belgium.

Zaman an shirya gudanar da shi ne a tsakanin Shugaban kasa da gwamnonin domin su tattauna a tsakaninsu a fitar da shugaban jam'iyya na kasa da kuma yankunan da za a raba sauran mukaman jam'iyya.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta sanar da cewa za a yi zaman a ranar Talata kwana hudu kafin ranar da aka shata gudanar da babban taro na kasa na APC.
Majiyar da jaridar Nation ta sakaya sunanta ya ce za a yi zaman a Talata kamar yadda aka tsara.