Kungiyar Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohi Ta Yi Gaisuwar Rasuwar Mahaifin Takwaranta na Zamfara
Shugaban hadaddiyar kungiyar ya kara da cewa, tun lokacin da yan bindiga dadi suka sace baban nasu tare da sauran iyalan gidan suka ci gaba da yin addu'a na ganin Allah ya kubutar dasu cikin sauki.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
A yau ne shugaban nin majalisun dokokin jihohin kasar nan a karkashin jagoran cin shugaban ta honorable Abubakar Y Suleman sun kai ziyarar ta'aziya ga shugaban majalisar hon Nasiru Mu'azu Magarya, bisa ga rashin mahaifin sa.
Da yake jawabi shugaban kungiyar kuma shugaban majalisar jihar Bauchi, honorabul Abubakar Y Suleman yace, sun zo a jihar zamfara domin su hadu da takwaran su da kuma gwamnatin jihar su yi masu gaisuwar ta'aziyar rashin da akayi na mahaifin su.
Yace sun shigo jihar ta zamfara ne duk da shawarwarin da aka basu na cewa akwai hadari zuwa wannan jihar, domin su yi gaisuwar ta'aziya ga shugaban majalisar dokoki da kuma gwamna Matawalle da sauran yan majalisun na jihar zamfara da kuma jama'ar jihar.
Shugaban hadaddiyar kungiyar ya kara da cewa, tun lokacin da yan bindiga dadi suka sace baban nasu tare da sauran iyalan gidan suka ci gaba da yin addu'a na ganin Allah ya kubutar dasu cikin sauki.
"A madadin dukkan shugaban nin majalisun dokokin jihohin kasar nan, muna mika sakon ta'aziyar mu ga me da rasuwar baban mu Alhaji Mu'azu sabom garin magaraya, ga gwamnati da jama'ar wannan jihar da fatar Allah yayi masa rahama."
Da yake mayarda jawabi, shugaban majalisar dokoki jihar ta zamfara honorabul Nasiru Mu'azu Magarya yayi yaba masu bisa ga wannan ta'aziyar da suka zo yi masu, ya kara da cewa gaskiyar magana lokacin da aka dauke mahaifin nasa, sunyi iya kokarin su domin su ga an kubutar da shi amma abun ya cutura.
"An dauke shi tun cikin watan takwas na wannan shekara ya zauna hannun su na tsawon wata biyu ko kasa da hakan, sai gashi Allah yayi nashi iko ya karbi rayuwar sa, da fatar Allah yayi masa rahama.
"Kamar yanda aka fada maku cewa akwai hadari zuwa zamfara abun ba haka yake ba, tunda gashi kun shigo kuma kinga kowa na walwala, kuna iya zuwa kananan hukumimi 14 dake jihar nan ba tare da tsangwama ba, adon haka gwamna Matawalle ya can canci yabo domin lokacin da yau karagar mulki baka iya zuwa koda karamar hukumar mulki daya saboda tsoron yan ta'dda."
Tawagar ta hadaddiyar kungiyar yan majalisun dokokin jihohin kasar da suka kawo gaisuwar ta'aziyar sun hada da shugaban nin majalisun dokokin jihohin Kano, Katsina, Bauchi, Kebbi da dai sauran su.
managarciya