Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Kano ta dakatar da ƴar fim, Sahma

Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Kano ta dakatar da ƴar fim, Sahma

Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano ta dakatar da Sahma M Inuwa daga shiga harkar film na tsawon shekara daya, tare da kwace shedarta ta zama halartacciyar yar film.

A wata sanarwar da jami'in yada labaran hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya aikawa manema labarai ya shaida cewa hukumar ta sha al'washin ba za ta sake tace duk wani film da Samha ta fito a ciki.

Wannan ya biyo bayan wasu korafe-korafe da al'umma su ka yi kan wani bidiyo da jarumar ta saki da ke nuna shigar da bata dace da koyarwar addinin musulunci ba, baya ga samunta da yin kalaman da basu dace ba.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta dakatar da Samha har tsawon shekara daya a wani mataki na tabbatar da bin dokoki tare da kara tsaftace masana'antar  Kannywood.