Tawagar Kamfen PDP Sun Samu Tarbo A Garin Tambuwal Cikin Sokoto
Gwamna Tambuwal da Uban Doma, sun Samu Gagarumin Tarbo daga Alummar Garin Tambuwal.
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
A Cigaba da Zagayen da jamiyyu ke yi dan neman goyon bayan masoyan su, A Sakkwato, Gwamnan jihar Rt Hon. Aminu Waziri Tambuwal matawallen Sakkwato,kana Dan takarar Sanata, ya samu Gagarumin tarbo a lokacin da ya ziyarci mahaifar sa ta Tambuwal, tare da Dan takarar Gwamnan Sokoto Malam Saidu umar Ubandoma, da sauran Yan takarar yankin
Dinbin magoya bayan jamiyyar PDP ce sukayi dafifi a wajen da akayi Taron da Kuma cikin Garin Tambuwal inda ake ta daga hannu da nuna goyon baya ga Yan takarar. A zaben da ya gabata Tambulawa sun Bada kuriu masu yawa ga Dan nasu, wanda masana suka tabbatar da shine silar zuwa zabe zagaye na Biyu
Gwamnan tare da rakkiyar matainakin sa, Hon. Munir muhd Dan iya,walin Sokoto, Daraktan yekuwar zaben ,Kuma tsohon mnista Yusuf Suleiman,tsohon minista, Kuma tsohon mataimakin Gwamna Muntari Shehu Shagari,daukacin Yan takarar yankin, Shugaban jamiyyar PDP ta Sokoto da sauran magoya bayan jamiyyar Maza da mata, da sauran su.
managarciya