Dukkan Inconclusive  Za'a Gudanar Da Su Bayan Kammala Zaben Gwamna--INEC

Dukkan Inconclusive  Za'a Gudanar Da Su Bayan Kammala Zaben Gwamna--INEC

 

Hukumar zabe mai zaman kanta waton INEC ta sanar da bayanin cewa dukkwan zabukkan da ba su kammala ba waton inconclusive za a gudanar da su bayan kammala zaben  gwamna da aka shata gudanarwa ranar Assabar 11 ga watan Maris na shekarar 2023.

Bayanin na kunshe ne cikin wata takarda da Fetus Okoye kwamitin yada labarai na hukumar zabe ya sanyawa hannu ke yawo a kafofin sada zumunta ya ce hukumar tana sane da wasu yankunan Sanatoci da majalisar wakillai da ba a kammala zaben su ba.

"Hukumar zabe tana tattara wuraren da zaben bai kammala ba don haka za a sanar da ranar gudanar da zaben sai dai za a yi hakan ne bayan kammala zaben Gwamna dana majalisar dokokin jiha".