Tambuwal Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Layin Sadarwa a Ƙananan Hukumomin Da Aka Rufe A Sakkwato

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya buƙaci gwamnatin tarayya data gaggauta cire dokar yanke hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 cikin 23 dake jihar.
Bayan zama a majalisar tsaro ta jiha kan harin da 'yan bindiga suka kai a garin Goronyo wanda ya lakume rayukkan mutane da dama gwamnatin jihar ta rubutawa gwamnatin tarayya a hukumance ta dakatarda rufe layukkan wayar sadarwa a kananan hukumomin da abin ya shafa a jiha.
Ya ce bude layukkan ya zama wajibi saboda jami'an tsaro sun koka rufewar na shafar gudanar da aikinsu cikin nasara.
Ya ce an riga an aikawa Ministan Sadarwa takardar neman duba lamarin na rufe layi da aka yi.