Hukumar Gudanarwar Kwalejin Ilmi Ta Shehu Shagari  Ta Aminta Da Buɗe Makarantar A Sakkwato

Hukumar Gudanarwar Kwalejin Ilmi Ta Shehu Shagari  Ta Aminta Da Buɗe Makarantar A Sakkwato

Daga Jabir Ridwan.

Bayan shafe tsawon lokaci a rufe, hukumar gudanarwar kwalejin ilmi ta Shehu Shagari dake nan Sakkwato a yayin taronta karo na 79 data gudanar yau ta aminta da sake bude kwalejin daga ranar Litinin 8 ga watan Ogustan 2022.

Idan dai za'a iya tunawa hukumar ta rufe kwalejin ne biyo bayan kisan wata daliba da ake zargi da yin  kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Wannan na kunshe ne cikin wani bayani da magakatardan kwalejin Mallam Gandi Asaray a fitar. 
Bayanin a saboda haka ya bukaci dukkanin daliban kwalejin dake karatun NCE da kuma Degree dasu je kwalejin a tsakanin ranar 8 zuwa 11 ga watan Ogusta domin rattaba hannu akan yarjejeniyar cewa ba zasu sake tayarda tasniya a kwalejin ba.