Hon. Abdussamad Dasuki: Idan Ka Ji Wane Ba Banza Ba

Yarima a Cibiyar Daular Usmaniyya, cikakken Basaraken da ke iya amsa sunan Basarake a kowace irin kasaitacciyar Masarauta a duniya, ɗan Sarkin Musulmi na 18, Ibrahim Dasuki CON, LLD D. Litt (Allah ya ci-gaba da lulluɓe shi da bargon Rahama) ya samu karramawar sarauta mai girma da daraja ta San-Turakin Sakkwato daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III a bisa ga muhimmiyar gudunmuwar ci-gaban Addini, taimakon al'umma da hoɓɓasar ƙwazon raya gidan Mujaddadi Shehu Ɗan-Fodiyo.  Tsohon ɗalibin kwalejin horas da Hafsoshin soji ta NDA, tsohon Manajan Bunkasa Harkokin Kasuwanci a Rukunin Kamfanin Dangote wanda ya jagoranci samun naira biliyan 10 a kowane wata a sashen siminti na Dangote/Obajana, Ɗan Majalisar Dokoki na Jiha da ya wakilci Tambuwal ta Gabas a 2011- 2015, Mai Shata Dokoki a Majalisar Wakilai ta Takwas 2015- 2019 kana Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa, Hon. Dasuki wanda a yau ke jagorantar Ma'aikatar Kudi a matsayin Kwamishina ya kafa tarihin sauke dukkanin nauyin da Mai Girma Gwamna Tambuwal ya ɗora masa ta hanyar baiwa maraɗa kunya. 

Hon. Abdussamad Dasuki: Idan Ka Ji Wane Ba Banza Ba
Hon. Abdussamad Dasuki

Hon. Abdussamad Dasuki: Idan Ka Ji Wane Ba Banza Ba

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar

Ƙwarewa da gogewa a sha'anin tattalin arziki, nasibi a harkar kasuwanci, naƙaltar siyasar ci-gaban al'umma, iya hulɗa da jama'a da jajircewar ganin al'umma ta samu kyakkyawar makoma, a sahun 'yan siyasa Honarabul Abdussamad Dasuki ya yi wa tsara ratar da sai dai su biyo sahu. 

Nagartaccen ɗan siyasar da ya zama abin koyi da kwatance ya bayar da cikakkiyar gudunmuwa ga ci-gaban Kasa da Jiha, inganta rayuwa da gina al'umma, samarwa matasa aiki da daukar nauyin karatu, tallafawa talakawa da 'yan Rabbana ka wadata mu tare da share hawayen marayu.

Hulɗa da zamantakewa, siyasance a Jihar Sakkwato an tabbatar da Hon. Abdussamad Dasuki yana sahun zaratan matasan 'yan siyasar da ke kamanta gaskiya, riƙon amana, dattako, halin girma da girmamawa tare da sanin ya kamata wadanda jama'a shaida ne yadda a sahun Kwamishinoni ya zama nagari na kowa.
 
Honarabul  Abdussamad Dasuki wanda babban jigo ne a siyasar aƙida ta ci-gaba da bunƙasar al'umma da jagoran raya Jihar Sakkwato, haziƙin gwarzon Gwamna, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta ya samarwa kansa suna wajen ɗora tubali da ginshiƙin cimma biyan buƙatar da ake buƙata a lokacin da ake buƙata ba tare da rashin biyan buƙatar da ba a buƙata ta rinjayi buƙatar da ake buƙata ba. 

Yarima a Cibiyar Daular Usmaniyya, cikakken Basaraken da ke iya amsa sunan Basarake a kowace irin kasaitacciyar Masarauta a duniya, ɗan Sarkin Musulmi na 18, Ibrahim Dasuki CON, LLD D. Litt (Allah ya ci-gaba da lulluɓe shi da bargon Rahama) ya samu karramawar sarauta mai girma da daraja ta San-Turakin Sakkwato daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III a bisa ga muhimmiyar gudunmuwar ci-gaban Addini, taimakon al'umma da hoɓɓasar ƙwazon raya gidan Mujaddadi Shehu Ɗan-Fodiyo. 

Tsohon ɗalibin kwalejin horas da Hafsoshin soji ta NDA, tsohon Manajan Bunkasa Harkokin Kasuwanci a Rukunin Kamfanin Dangote wanda ya jagoranci samun naira biliyan 10 a kowane wata a sashen siminti na Dangote/Obajana, Ɗan Majalisar Dokoki na Jiha da ya wakilci Tambuwal ta Gabas a 2011- 2015, Mai Shata Dokoki a Majalisar Wakilai ta Takwas 2015- 2019 kana Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa, Hon. Dasuki wanda a yau ke jagorantar Ma'aikatar Kudi a matsayin Kwamishina ya kafa tarihin sauke dukkanin nauyin da Mai Girma Gwamna Tambuwal ya ɗora masa ta hanyar baiwa maraɗa kunya. 

A Majalisar Dokoki ta Jiha da Majalisar Waƙilai ta ƙasa zubi na Takwas, Hon. Abdussamad Dasuki ya gudanar da ingantacce kuma karɓaɓɓen waƙilcin da ya shiga cikin kundin tarihin sahihin waƙilcin da jama'a suka yaba ta yadda a yau bayan bankwana da majalisun biyu jama'a na cikin ƙishirwa da kewar rabuwa da amintaccen waƙilcinsa nagari wanda a yau a ke ci-gaba da ribanta da ayyukan alhairi da ingantattun ƙudurori da dokokin da ya gabatar. 

Hon. Abdussamad Dasuki na hannun daman Aliko Dangote, attajiri mafi kuɗi a Afurka a matsayinsa na ƙwararren masani tattalin arziki wanda ya san ciki da wajen harkokin kuɗi, ya assasa shiraruwa da tsare-tsare masu alfanu tare da dora Ma'aikatar Kuɗi ta Jiha saman tsarin kyawawan hanyoyi da nasarorin da za a jima a na cin moriya wanda hakan ya biyo bayan zamansa jagoran da ya nuna a fili irin yadda ya kamata shugaba ya zama kuma ya kasance. 

A wannan shekarar ce Jihar Sakkwato ta kafa tarihi da samu lambar yabo da jinjinar musamman daga Bankin Duniya ta hanyar zama ta daya a Nijeriya bakidaya a shirin Gwamnatin Jiha na tsaftace tu'ammali da kudade (SFTAS) ta hanyar kaiwa mataki na 14/15 tare da samun tallafin tsabar zunzurutun kudi har naira biliyan takwas wato Dala miliyan 22 daga Bankin Duniya kan aiwatar da gaskiya da adalci a harkokin kudade wanda hakan karara ya nuna Mai Girma San-Turaki ba kyalle ba ne babban bargo ne!

Jim kadan bayan wannan nasarar irinta ta farko sai ga Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma'aikatar Kudi ta Kasa ta bayyyana Jihar Sakkwato a matsayin ta daya a kasar nan wajen bin tsarin gaskiya da adalci a hada-hadar kudade tare da samun tsabar kudi naira biliyan shida, 6.612 wanda hakan ya sa Jihohi da dama kara sallamawa Gwamnatin Mutawallen Sakkwato tare da koyi a kan kyawawan jagorancin Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya. 

Gwamnatin Tambuwal wadda ta samu nasarar toshe badakalar naira miliyan 500 da ke sulalewa a kowane wata daga albashin ma'aikata da gano ma'aikatan bogi sama da 1, 000, wadda tuni ta sake fitowa da tsarin takardar biyan albashi domin wanzar da adalci da kawar da duk wata rashin gaskiya, a yanzu haka ita ce kan gaba wajen biyan albashin ma'aikata a kowane wata a fadin kasar nan wadda a wasu jihohi ma'aikata da dama ke kukan bin bashin albashin wata da watanni, haka ma ta yi nisa wajen biyan kudaden garatuti baya ga biyan kudaden fansho a kodayaushe.

Haka ma Jihar Sakkwato ta shiga sahun farko wajen cika ka'idojin huldar kudade na wata-wata da biyan kudaden da ake bin ta bashi a 2019 kamar yadda ofishin Babban Akawun Gwamnatin Tarayya da Ofishin Kula da Bashi na Kasa ya bayyana. Bugu da kari Jihar Sakkwato ta kai kashi 93 cikin 100 na cika sharuddan tu'ammalli da bin ka'idar tafiyar da kudade kamar yadda Bankin Duniya da cibiya mai zaman kanta ta tabbatar da ingancin ayyuka da ke a Bankin Duniya ta tabbatar. 

Gwamnatin Tambuwal wadda ta kara bunkasa ayyukan Hukumar Tattara Haraji a 2019 da sababbin hanyoyin bunkasa kudaden shiga a yanzu haka ta karfafa tare da inganta ayyukan Hukumar Tattara Haraji ta Jiha (SOIRS) ta hanyar sabbin tsare-tsare, fitowa da sababbin dokoki, toshe sulalewar haraji, hada kudaden haraji a waje daya, tabbatar da shigar haraji a asusun Gwamnati da daukar sababbin ma'aikata domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu tuni ta samu dimbin ci-gaba da sauyi mai ma'ana a harajin da ake karba. 

"Gwamnatin mu za ta mayar da hankali ga kudaden harajin da ake samu wajen yi wa jama'a ayyuka da su. A kakashin jagorancin mu babu siyasa a cikin haraji kuma ba za a samu handama da babakere ba, za mu yi iyakar kokarin rike amanar dukiyar jama'a da yardar Allah." Cewar Tambuwal, Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP a wani taron kwana daya kan inganta Haraji a Sakkwato.

A bisa ga yadda kusan dukkanin Jihohin Nijeriya idan ban da kalilan suka dogaro kacokam ga kudaden kason Gwamnatin Tarayya na wata-wata wajen tafiyar da lamurransu da fargabar da ke akwai ta kasa iya rike kai idan babu kason tallafin; Gwamnatin Sakkwato a bisa ga tunani da hangen nesa ta tsara hanyoyin da za ta fara biyan albashi daga Haraji a shekaru biyu masu zuwa wanda wannan babban ci-gaba ne maras misaltuwa wanda hatta 'yan adawa sai da suka yaba. 

"Nan da shekaru biyu Jihar Sakkwato za ta fara biyan albashi a harajin da ta ke tarawa. Zuwa shekarar 2023, Jihar Sakkwato za ta zama jiha ta farko a Nijeriya da za ta rika biyan albashin ma'aikata daga harajin da take karba na jiha." In ji Hon. Dasuki wanda ya samu karramawar Gwarzon Kwamishina a 2020.

Masani tattalin arziki kana tsohon Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa, Oseni Elemah ya bayyana cewar jinjina da yabon da Gwamnatin Tambuwal ta samu daga Bankin Duniya da ci-gaban da aka samu a fannin haraji sun samu ne a dalilin hobbasar kwazon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da jajirctaccen Kwamishinan Kudi, Hon. Abdussamad Dasuki wadanda suka dora Jihar a hanyar tudun mun tsira kamar yadda ya bayyana a taron horas da sababbin ma'aikatan Hukumar Tattara Haraji a watannin baya. 

Dukkanin wadannan nasarorin da aka samu da wadanda ake samu ba abin mamaki ba ne bisa la'akari da salon mulkin Gwamna Tambuwal na gaskiya da adalci wanda hawansa mulki zuwa yau ya ciri tuta wajen shayar da al'umma romon mulkin Dimokuradiyya ta hanyar kawar da matsalolinsu da inganta jin dadin su tare da aiwatar da muhimman ayyukan da suka yi tasiri a dukkanin fannoni ta yadda al'ummar Arewaci da Kudanci ke yi masa fatar zama Shugaban Nijeriya a 2023 domin kawar da gurbataccen shugabanci da  matsalolin da Gwamnatin 'canji' ta haddasa tare da dawowa da Kasar nan saman turba madaidaiciya. 

Alkalamin Sidi Umar ya rubuto ne daga Guiwa, Karamar Hukumar Wamakko, Jihar Sakkwato.